Kantoman Tudun wada Dr. Umar isah rugu-rugu ya jagoranci raban tallafin kudi naira dubu hamsin ga mata 100 domin suja jali a tudun wada.
Kantoma ruko na karamar Hukumar tudun wada Dr. Umar isah rugu-rugu ya yabawa gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin mai girma gwamna Alh. Abba kabir yusuf bisa yadda suke kokarin raba irin wannan tallafin ga Alumma duba da halin matsin rayuwa da Alumma suka tsinci kansu ciki.
Ya bayyana hakanne a yayin taron kaddamar da rabon tallafin kudi na jali ga mata wanda gwamnati kano ta bayar arabawa mabukata dake a karamar Hukumar ta tudun wada.
Dr. Umar isah rugu rugu yakara da cewa ” An baku wannan jali badan komai ba sai domin aje acigaba da gudanar da sanao’i wadanda basa sanaar kuma sunemi sanaoin dazasuyi domin kowa yasamu dogaro dakansa kuma muna fatan zakuyi dukkanin maiyuwa wajen amfanar dakanku kuma munafatan wannan tallafin zaizomo silar arzin ku.
Daga karshe rugu-rugu yaja hankalin Alummar yakin musamman wadanda basu samu a wannan karon ba suyi hakuri wannan shine karon farko kuma zaa cigaba da bayar da irin wadannan tsare tsaren anan gaba .










