• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Khadija Maitaya by Khadija Maitaya
August 29, 2026
Reading Time: 1 min read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
468
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Wani matashi mai suna Abdul’azi Dan Asalin Unguwa Uku, mazaunin Ƙaramar Hukumar Garun-Malam ta Jihar Kano, ya jikkata wata dattijuwa mai suna Hajiya Sahura Kura, mai kimanin shekaru 75, tare da yi mata barin makauniya.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne bayan dattijuwar ta hana matashin shiga ɗakin karɓar haihuwa, bisa dokar da ta hana maza shiga sashen kula da mata masu haihuwa.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Hajiya Sahura ta shafe kimanin shekaru 35 tana aiki a sashen kula da mata masu karɓar haihuwa a Babban Asibitin Ƙaramar Hukumar Kura. Mahukuntan asibitin sun kama wanda ake zargin a lokacin da yake ƙoƙarin ci gaba da dukan dattijuwar.

Shugaban asibitin, Dr. Muktar Wudil, ya umarci sakataren asibitin, Aliyu Isma’ila Kiru, da ya miƙa wanda ake zargin ga rundunar ’yan sandan Kura domin gudanar da bincike.

Bayan kammala bincike, ’yan sandan sun gurfanar da Abdul’azi a gaban Kotun Majistare ta Ƙaramar Hukumar Kura, ƙarƙashin jagorancin Chief Magistrate Muhammad Alhaji Isa. Mai gabatar da ƙara, Inspector Nasiru Abubakar Dansakkwato, ya gabatar da takardar tuhuma a gaban kotun.

Bayan an karanta masa tuhumar, alkalin kotun ya tambaye shi ko ya aikata laifin, inda wanda ake zargin ya amsa cewa ya aikata laifin.

Alkalin ya yi masa nasiha tare da tunasar da shi irin shekarun dattijuwar da kuma tsawon lokacin da ta shafe tana yi wa al’umma hidima. Sai dai saboda ƙarancin lokaci da kuma halin da wanda abin ya shafa ke ciki, kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 17 ga Satumba, 2026.

Kotun ta kuma bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a hannun jami’in gidan yari da gyaran hali, Hasan Muhammad Gambo Gwaneri, har zuwa ranar ci gaba da sauraron shari’ar.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

China Da India Sun Gargadi Russia Kan Shirin Amfani Da Nuclear A Kan Ƙasar Ukrain

Next Post

Kotun Kiru Ta Aike da Matashi Gidan Yari Bisa Zargin Sauya Bayanan Banki

Khadija Maitaya

Khadija Maitaya

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Shugaban kasar Türkiye ya mika daruruwan gidaje ya ya gina wa wadanda girgizar kasa ta shafa

Shugaban kasar Türkiye ya mika daruruwan gidaje ya ya gina wa wadanda girgizar kasa ta shafa

February 6, 2024
Kungiyar Cigaba Tagwaye Ta Jihar Kano Mika Godiya Ga Gwamna Abba Kabir Yusuf Da Kuma Gwamnatin Saudiyya

Kungiyar Cigaba Tagwaye Ta Jihar Kano Mika Godiya Ga Gwamna Abba Kabir Yusuf Da Kuma Gwamnatin Saudiyya

September 13, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media