Sarkin Zurmi na Jihar Zamfara, Alhaji Bello Suleiman, ya rasu bayan shafe shekaru biyar yana kan karagar mulki.
Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a ranar Litinin da yamma a Asibitin
Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, kamar yadda wata sanarwa daga fadar masarautar ta bayyana.
Alhaji Bello Suleiman ya zama Sarkin Zurmi ne a shekarar 2021, bayan ya gaji kawunsa, Alhaji Abubakar Atiku, wanda gwamnatin jihar ta cire daga mukaminsa a wannan shekarar, kafin daga bisani aka tabbatar da tsige shi a watan Afrilun 2022.
An cire Atiku daga sarautar tare da Sarkin Dansadau, Hussaini Umar. An zarge su da alaka da ‘yan bindiga da kuma tsoma baki cikin ayyukan jami’an tsaro.
Daga bisani, tsohon Sarkin Zurmi, Abubakar Atiku, ya rasu a wani asibiti da ke ƙasar Masar.









