• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Khadija Maitaya by Khadija Maitaya
August 7, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home KOTU
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Kotun Majistare da ke Kwanar Dangora, a ƙaramar hukumar Bebeji ta Jihar Kano, ta yanke wa wata matar aure mai suna Maimuna hukunci bayan samunta da laifin watsa tafasasshen ruwa ga kishiyarta, Zainabu.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a unguwar Rimi Bakin Kwata da ke Kwanar Dangora, inda ake zargin Maimuna ta kai wa sabuwar amaryar harin sakamakon rikicin cikin gida da ake dangantawa da kishi. An ce Zainabu ta samu munanan ƙonewa a sassan jikinta, lamarin da ya sa makwabta suka garzaya domin kai mata ɗauki kafin a kai ta asibiti.

RelatedPosts

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar (ADC) Na Kasa

Kotun Koli ta yanke hukuncin kan rikicin jam’iyyar PDP

Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi

A gaban kotu, ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Sajan Aminu Muhammad Ciromawa, ya gabatar da takardar tuhuma tare da shaidu da suka haɗa da rahoton asibiti da takardun magunguna. A zaman farko, wacce ake zargi ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi.

Sai dai a zaman da aka koma domin ci gaba da shari’ar, Maimuna ta samu lauya, Barista Ibrahim Salihu Faki, wanda ya nemi a sake karanta mata tuhumar. Bayan an sake karanta ta, Maimuna ta musanta aikata laifin, yayin da lauyanta ya nemi a ba ta beli. Sai dai mai gabatar da ƙara ya roƙi kotu ta yi hukunci bisa amsar laifin da ta yi tun farko.

Bayan nazarin hujjoji da takardun asibiti, Babban Alƙalin Kotun, Chief Majistare Muhammad Alh. Isa, ya yanke wa Maimuna hukuncin zaman watanni huɗu a gidan gyaran hali ba tare da zaɓin tara ba. Haka kuma, kotun ta ci ta tarar naira dubu ɗari takwas da arba’in. Idan ta gaza biya, za ta ƙara yin shekara biyu a gidan gyaran hali.

Alƙalin ya bayyana cewa tana da damar ɗaukaka ƙara cikin wa’adin wata guda. Bayan kammala shari’ar, jami’an gidan gyaran hali suka karɓi wacce aka yankewa hukuncin domin aiwatar da umarnin kotu.

A nasa ɓangaren, lauyan wacce aka yankewa hukunci, Barista Ibrahim Salihu Faki, ya shaida wa manema labarai cewa za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ta yanke.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Atiku Ya Koka Bayan Da Aka Tura Masa Kuɗi A Asusunsa Ba Tare Da Saninsa Ba

Next Post

13 People, Including Children, Rescued After Building Collapses in Dan Dishe, Kano

Khadija Maitaya

Khadija Maitaya

RelatedPosts

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar  (ADC) Na Kasa
KOTU

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sanata David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban Jam’iyyar (ADC) Na Kasa

by aksam
April 30, 2026
Yau Ake Sa Ran Kotun Koli Ta Najeriya Zata Yanke Hukunci A Yau Kan Rikicin Shugabancin  Jam’iyyar ADC A Matakin Kasa
KOTU

Kotun Koli ta yanke hukuncin kan rikicin jam’iyyar PDP

by aksam
April 30, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi
KOTU

Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi

by aksam
April 22, 2026
Yau Ake Sa Ran Kotun Koli Ta Najeriya Zata Yanke Hukunci A Yau Kan Rikicin Shugabancin  Jam’iyyar ADC A Matakin Kasa
KOTU

Yau Ake Sa Ran Kotun Koli Ta Najeriya Zata Yanke Hukunci A Yau Kan Rikicin Shugabancin Jam’iyyar ADC A Matakin Kasa

by aksam
April 22, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Die Zukunft des Online-Glücksspiels in Deutschland: Regulierung, Trends und Herausforderungen

April 21, 2025
Asarar da kanawa da yan Arewa suka yi a ranar farko ta zanga-zangar Kano

Asarar da kanawa da yan Arewa suka yi a ranar farko ta zanga-zangar Kano

August 3, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media