Daga Hassan Umar Gwammaja
Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Portugal, Cristiano Ronaldo, ya auri abokiyar zamansa na dogon lokaci, Georgina Rodríguez, a ranar Talata.
An gudanar da bikin auren ne a garin Cascais, wani wurin yawon buɗe ido da ke Portugal, kamar yadda wakilan ɗan wasan suka tabbatar.
Ronaldo da Georgina sun shafe shekaru suna tare, kuma suna da ’ya’ya 5 tare.










