Mai magana da yawun Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), Janar Hossein Mohebbi, ya bayyana cewa Amurka a halin yanzu ba ta da wani jirgin ruwan yaƙi da ke cikin Tekun Fasha.
Mohebbi ya ce kafin yaƙin Ramadan, Amurka tana da jiragen ruwan yaƙi tsakanin 30 zuwa 40 a yankin, amma a yanzu babu ko guda ɗaya da ke cikin Tekun Fasha. Rahotanni sun tabbatar da cewa Mohebbi shi ne sabon kakakin IRGC.
Ya kuma yi gargaɗin cewa idan wata barazana ta sake tasowa ga Iran, abubuwan more rayuwa da makamashi da suka haɗa da dubban cibiyoyin samar da wutar lantarki, manyan bututun makamashi da sauran tsarin sadarwa da ke haɗe da intanet a duniya na iya fuskantar barazana.
A cewarsa, dabarun yaƙin Amurka sun dogara ne kan iya yaƙi a fannoni da dama a lokaci guda. Ya ce rage yawan makamai da ƙarfin sojin Amurka, ko da a yankunan da ke nesa kamar tsakiyar Tekun Pasifik, na iya haifar da babbar barazana ga Washington wajen tunkarar Rasha da China, da kuma sauran wuraren da Amurka ke ganin suna da barazana.
Maganganun na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun takaddama tsakanin Iran da Amurka kan Tekun Hormuz, inda Iran ta dage cewa ba za a dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa yadda ya kamata ba sai Amurka ta amince da wasu sharuddan Tehran









