AKSAMMEDIA KANO — A lokacin da tsarin samar da fasfo ke fuskantar sauyin daga Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta ce yana da nufin mayar da aikin buga littafin fasfo zuwa cibiyar Abuja, lamarin ya jawo sabon tambaya daga Arewa: ina muryar waɗanda aka zaɓa domin kare muradun al’umma?
Sheikh Muhammad Nasir Yahya ya yi wannan tambayar ne a hudubar Juma’ar da ya gabatar a Masallacin Juma’a na Sasif da ke Unguwar Gwagwarwa, Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Kano, inda ya bayyana matakin da ya shafi wasu cibiyoyin fasfo a matsayin wani ƙalubale da ya kamata shugabannin siyasa da wakilan jama’a su duba da muhimmanci.
Malamin ya ce idan har yankunan Arewa sun samu kaso mai yawa daga cikin cibiyoyin da aka shigar da su cikin sabon tsarin, ya kamata gwamnonin Arewa, sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai su tashi tsaye domin kare muradun al’ummar da suka zaɓe su. Ya tunatar da su cewa rantsuwar da suka yi da Alƙur’ani Mai Girma lokacin karɓar amanar wakilci ba abin ado ba ce, illa nauyi ne da ya kamata ya bayyana a aikace.
Ya kuma jefa tambaya mai nauyi ga wakilan jama’a: “Idan aka ɗauki matakin da zai iya ƙara wa jama’a wahala, amma waɗanda aka zaɓa domin kare muradunsu suka yi shiru, shin wannan ba alamar gazawar wakilci ba ce?”
Sai dai NIS ta jaddada cewa ba ta rufe ofisoshin karɓar bayanan masu neman fasfo ba; abin da aka sauya shi ne tsarin production/personalisation, inda ake samar da littafin fasfo a cibiyar Abuja, yayin da cibiyoyin yankuna ke ci gaba da karɓar bayanan biometric na masu neman fasfo.









