• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kwamishina wayya yayi gargadi akan masu yada jita jita akan auren gata a Kano

Khadija Maitaya by Khadija Maitaya
August 11, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

By:Khadija Muhammad Maitaya

Date:August 11,2026

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga al’ummar jihar da su guji yada jita-jita da bayanan da ba su da tushe, musamman kan shirin Auren Gata da gwamnatin jihar ta gudanar.

Kwamishinan ya yi wannan kiran ne yayin wata ganawa da ƙungiyar matasan Limaman Masallatan Juma’a na Kano, inda ya jaddada muhimmiyar rawar da limamai ke takawa wajen wayar da kan jama’a da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Waiya ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mutane ke yaɗa hotunan wasu dattawa a kafafen sada zumunta, tare da ikirarin cewa an ɗaura musu aure a ƙarƙashin shirin Auren Gata na gwamnatin jihar.

A cewarsa, bincike ya nuna cewa wasu daga cikin mutanen da ake yaɗa hotunansu tsofaffin jami’an Hisbah ne da suka yi ritaya daga aiki, ba sababbin Angwayen da aka ɗaura wa aure a ƙarƙashin shirin Auren Gata ba ne.

Ya ce yaɗa bayanai ba tare da tabbatar da sahihancinsu ba na iya haifar da ruɗani, rashin fahimta da kuma tayar da hankalin jama’a.

Kwamishinan ya buƙaci al’umma da su riƙa tantance sahihancin duk wani bayani kafin su yaɗa shi, tare da mayar da hankali wajen yaɗa saƙonnin da za su amfani al’umma.

Ya kuma jaddada cewa limaman Masallatan Juma’a suna da babbar rawar da za su taka wajen wayar da kan jama’a kan illolin jita-jita, da kuma ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’ummar Kano.

Kwamared Waiya ya ce shirin Auren Gata yana da muhimmiyar manufa, wato tallafa wa waɗanda aka shirya wa auren tare da rage musu nauyin kuɗaɗen da ke tattare da gudanar da aure.

Ya ƙara da cewa ya kamata limamai da sauran masu ruwa da tsaki su ci gaba da wayar da kan jama’a kan manufar shirin, domin kauce wa yaɗa bayanan da ba su dace ba.

Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi kira ga al’ummar Kano da su haɗa kai da gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna, tare da tabbatar da cewa duk wani bayani da za a yaɗa sahihi ne kuma mai amfani ga al’umma.

A nasa jawabin shugaban Ƙungiyar Matasan Limamai Masu Son Ci gaban Jihar Kano ya jaddada goyon bayansu ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa yadda yake gudanar da ayyuka a jihar.

Ya ce sun kawo wannan ziyara ne domin ƙarfafa tafiyar mai girma Gwamna, bisa yadda ya gudanar da shirin Auren Gata a jihar, da kuma ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa a faɗin jihar Kano.

Haka zalika, ya ƙara da cewa sun kawo ziyarar ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Abdullahi Waiya, bisa yadda yake shiga cikin al’amuran malamai a jihar. Ya ce a shirye suke su ci gaba da yi wa gwamnatin addu’a domin ci gaban Jihar Kano.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

UAE Ta Zuba Dala Biliyan 168 a Afirka

Next Post

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Khadija Maitaya

Khadija Maitaya

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Majalisar dattawa ta sanar da rashin daya daga cikin yayan ta

Majalisar tarayya na duba yuwuwar kara jihohi biyu a yankin kudu maso yamma

October 23, 2024

Using Bitcoin at makispin casino: A Complete Guide

April 22, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media