Daga: Hassan Umar Gwammaja
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya ɓarke ne tun bayan da Nafiu Bala Gombe ya ayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa, lamarin da ya janyo saɓani a cikin jam’iyyar.
A gefe guda kuma, David Mark shi ma yana iƙirarin shugabancin jam’iyyar, inda yake samun goyon bayan wasu jiga-jigan ADC.
Ana kallon hukuncin da kotun za ta yanke a yau a matsayin wanda zai kawo ƙarshen wannan rikici, tare da fayyace sahihin shugabanci, bayan da saɓanin ya fara kawo cikas ga tafiyar da harkokin jam’iyyar.









