Daga: Hassan Umar Gwammaja
Hakan na cikin sanarwar da mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Malam Mukhtar Gidado ya fitar a ranar Laraba 22 ga watan Afrilu 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin bin tanade tanaden dokar zaɓe ta shekarar 2026, wadda ta tanadi cewa duk mai riƙe da muƙamin gwamnati da ke son shiga zaɓe dole ne ya sauka daga muƙaminsa kafin lokaci
Haka kuma, an umarci waɗanda abin ya shafa da su miƙa kadarorin gwamnati da ke hannunsu tare da mika ayyukansu ga waɗanda suka dace a ma’aikatunsu. Gwamnatin ta gode musu bisa gudunmawar da suka bayar tare da yi musu fatan alheri a ƙoƙarinsu na neman muƙaman zaɓe.










