Rahotanni daga jaridar The Wall Street Journal, sun bayyana cewa ƙasar China ta rufe wasu manyan yankuna na sararin samaniya a gabar tekun gabashinta na tsawon kusan kwanaki 40.
Rahoton ya ce wannan mataki ya fi tsawon lokutan da aka saba na rufe sararin samaniya domin atisayen soja, kuma ba a bayyana dalilin hakan ba.
Yankunan da aka takaita suna kusa da Tekun Yellow da kuma Tekun Gabashin China, kuma suna nesa da Taiwan.












