• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

IRGC ta harbo jiragen Amurka da suka yi kokarin cetar wani pilot da Iran ta Kama

aksam by aksam
April 5, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

AKSAMMEDIA-KANO– Rundunar sojin Iran ta sanar da cewa ta dakile wani yunkuri da Amurka ta yi na ceto wani matukin jirgi da ya fadi, inda aka lalata jiragen sama da dama ciki har da jiragen helikwafta na Black Hawk da kuma jirgin daukar kaya na soja a wani samame da aka kai a kudancin Isfahan.

Mai magana da yawun hedikwatar Khatam al-Anbia Central Headquarters ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 5 ga Afrilu, inda ya ce rundunar sojin Iran ta lalata wasu jiragen saman Amurka a kudancin Isfahan, tare da dakile wani yunkuri na cetar wani matukin jirgin yaki na Amurka da ya fadi.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Ya ce lamarin ya biyo bayan yunkurin da sojojin Amurka suka yi na kutsawa cikin tsakiyar Iran domin fitar da matukin jirgin.

Kakakin ya kara da cewa wani hadin gwiwa tsakanin rundunar sararin samaniya da ta kasa, tare da dakarun sa-kai na Basij da jami’an tsaro, ya yi nasarar dakile hare-haren jiragen da ke shigowa tare da tarwatsa su.

Ya bayyana cewa an lalata jiragen makiya da dama, yana mai cewa wannan wani sabon koma baya ne ga Amurka, inda ya kwatanta da gazawar Operation Eagle Claw a watan Afrilu na shekarar 1980.
Har ila yau, ya ce shugaban Amurka Donald Trump ya yi kokarin rage girman lamarin ta hanyar wallafa sako a shafukan sada zumunta yana mai cewa an gudanar da wani aiki na musamman domin ceto matukin jirgin.

Mai magana da yawun ya jaddada cewa kokarin makiyan ya ci tura ne sakamakon hadin kai da saurin daukar mataki na rundunar Iran, ciki har da Islamic Revolutionary Guard Corps, rundunar soji, dakarun Basij da kuma jami’an ‘yan sanda.

Ya kara da cewa jiragen da aka lalata sun hada da helikwafta biyu na Black Hawk da kuma jirgin daukar kaya na soja nau’in C-130, wadanda aka harba kuma suka kama da wuta a kudancin Isfahan.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

DA DUMI-DUMI: China ta rufe wasu bangarori a sararin samaniyar ta

Next Post

Tsagaita wuta na kwanaki 45 ba ya cikin manufofin Iran: TNA

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

NNPC ya magantu kan zagonkasa da ya gano ana yi masa

NNPC ya magantu kan zagonkasa da ya gano ana yi masa

June 27, 2025

The Advantages of Joining Blockspins Casino’s VIP Program

April 21, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media