• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Khadija Maitaya by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Hukumar hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen rundunar Kano ta gudanar da wani samame a tsohuwar Jami’ar Bayero Kano (BUK Old Site), inda ta kama mutane shida da ake zargi da hannu a harkokin miyagun kwayoyi tare da rusa wasu maboyarsu.

Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar ta dauki wannan mataki ne biyo bayan wata korafi a hukumance da mahukuntan jami’ar Bayero Kano suka gabatar mata.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sadi Muhammad maigatari ya sanyawa hannu.

A karkashin shirin “Operation Sharar Mafaka”, jami’an NDLEA sun kai samame domin fatattakar mutanen da suka mayar da wasu sassan harabar jami’ar wajen safarar da kuma shan miyagun kwayoyi.

A yayin samamen, an kama mutane shida da ake zargi, tare da kwace wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen gudanar da wadannan haramtattun ayyuka, inda aka lalata su domin hana ci gaba da amfani da su.

Da yake jawabi kan nasarar aikin, shugaban rundunar ta NDLEA a Kano , CN DY Lawal, ya ce wannan mataki na nuna kudirin hukumar wajen tabbatar da samar da muhalli mai tsabta daga miyagun kwayoyi domin dalibai, ma’aikata da iyalansu su gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba. Za mu ci gaba da fatattakar dukkan maboyar miyagun kwayoyi a karkashin Operation Sharar Mafaka,” in ji shi.

Har ila yau, wannan samame ya nuna muhimmancin hadin gwiwa tsakanin NDLEA da hukumomin ilimi, inda kai rahoton da wuri da hadin kan jami’ar ya taimaka wajen daukar mataki cikin gaggawa domin kawar da barazanar da ke addabar tsaron harabar makaranta da al’umma baki daya.

Hukumar NDLEA ta Kano ta sake gargadin duk wanda ke amfani da cibiyoyin gwamnati ko na ilimi wajen safarar ko shan miyagun kwayoyi da cewa ba za a lamunci irin wadannan ayyuka ba. Har ila yau, ta bukaci al’umma da cibiyoyi da su rika kai rahoton duk wani abu da ake zargi domin gano sauran maboyar masu laifi da kuma kawar da su baki daya

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Ya Koma Jam’iyyar National Democratic Congress (NDC) A Hukumance; Inda Ya Karɓi Katin Zama Mamba Na Jam’iyyar

Next Post

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Khadija Maitaya

Khadija Maitaya

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu Zai Bar Kasa Zuwa Kasar Faransa

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu Zai Bar Kasa Zuwa Kasar Faransa

August 18, 2024
Matashin da ya taso dago Adamawa zuwa jihar Katsina a Keke ya yaba wa gwamnan Kano bisa manyan aikace-aikace

Matashin da ya taso dago Adamawa zuwa jihar Katsina a Keke ya yaba wa gwamnan Kano bisa manyan aikace-aikace

August 1, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media