Daga Hassan Umar Gwammaja
Inda al’ummomi daban-daban suka hallara domin nuna haɗin kai, zaman lafiya, da zumunci ta hanyar wasanni.
A madadin Majalisar Gundumar Kwahu West, an bayar da lambobin yabo da kofin gasar domin tallafawa wannan muhimmin shiri.
Haka kuma, an bayyana godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudummawa wajen nasarar gasar, musamman Barracks Base, Nananom, Life FM, da kwamitin shirya gasar.
A ƙarshen fafatawar, Team Asante Kramo ta zama zakara bayan ta nuna ƙwazo, haɗin kai, da bajinta a duk tsawon gasar. An yaba wa ‘yan wasan da masu horar da su saboda irin namijin ƙoƙarin da suka yi wanda ya kai su ga samun nasara.
Da yake jawabi a yayin da aka kammala gasar wakilin Majalisar Gundumar Kwahu West Hon. Tanimu Haliru ya taya Team Asante Kramo murnar lashe kofin gasar, tare da yaba wa dukkan ƙungiyoyin da suka halarta saboda gudummawar da suka bayar wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai, da ruhin wasanni a tsakanin al’umma.
Masu shirya gasar sun bayyana cewa irin waɗannan shirye-shirye na taimakawa wajen ƙarfafa zumunci da fahimtar juna tsakanin kabilu daban-daban, tare da samar da dama ga matasa su nuna hazakarsu a fagen wasanni.










