Dan Wasan Kwallon Kafa Dan Asalin Kasar Portugal Ronaldo Ya Zaman Dan kwallon da yafi kowa kudi a jerin ‘yan kwallon
A cewar Bloomberg, Ronaldo, ya zama ɗan wasa na farko a tarihin ƙwallon ƙafa da ya mallaki Dala biliyan ɗaya na dukiya.
Matakin na zuwa ne bayan kwantiragin da ya ke da shi mai tarihi da ya kulla a kungiyarsa ta Al-Nassar da ke kasar Saudiyya.
Mai shekaru 40, ya sabunta kwantiragin na sa, da zai sa ya samu fam miliyan 492 cikin shekaru biyu masu zuwa.
Kuma a jumlace kudin da zai samu na kwantaragin, ya sanya darajar dukiyarsa ta karu zuwa dala biliyan 1.4, wato kimanin fam biliyan 1.045.












