• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Kungiyar direbobi na Bus-9 sun koka da nadin sabbin shugannin NURTW na jihar kano

aksam by aksam
March 17, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
469
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Kungiyoyin Direbobin Motocin haya da dama a jihar Kano, Sun bayyana rashin jin dadinsu bisa kin sanya sunan Alh.Abdullahi Isah daga cikin jagororin da aka kaddamar Karkashin ma’aikatar Sufuri na Kungiyar NURTW ta jihar Kano domin Shugabantar Kungiyar a jihar Kano.

Sakataren Kungiyar NURTW Bus 9 Malam Kato,Alh. Garba ne ya bayyana haka a wata zantawa da yayi da Manema labarai anan Kano.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Yace, Kwamishinan harkokin Sufuri na jihar Kano,Hon.Muhammad Ibrahim Diggol ya kamata yayi duba na musamman domin Neman hanyoyin magance Matsalolin dake Kunshe a cikin Kungiyar NURTW ta Kasa Reshen jihar Kano.

Sakataren ya Kara da cewa,Akwai Kungiyoyin Sufuri da Wanda da ba ma na Sufuri ba,a jihar Kano, Musamman na Kananan Hukumomi Sun amfana da yawa akan taimakon da Alh.Abdullahi Isah yake bayarwa,Amma,Abun Mamaki Kwamishinan harkokin Sufuri na jihar Kano, Muhammad Ibrahim Diggol yayi Kitso da Kwarkwata cikin Shugabannin da aka Rantsar a Helkwatar Kungiyar NURTW ta jihar Kano.

Wata Kungiyar Matasan Direbobi ta Kananan Hukumomi 44 a nan jihar Kano, ta yi mutukar nuna damuwarta dangane da cushen da ake zargin an yi cikin kunshi Shugabancin da ma’aikatar ta Sufuri tayi,Wanda hakan yakan fitar da wasu ‘Ya’yan jam’iyya daga cikin jamiyya da Kungiyoyin dake hidimtawa alummar jihar Kano.

To,sai dai kuma, idon Gwamnatin jihar Kano da masu ruwa da tsaki a fannin harkokin Kungiyoyin Sufuri, basu dauki matakai ba,wasu daga cikin ‘Yan’jamiyyun za su rika ficewa daga jamiyya, Musamman ta NNPP dake mulki a jihar Kano kamar yadda Kungiyar Matasan Direbobi ta bayyana a cikin wata takardar Shawara da ta aikewa Kwamishinan harkokin Sufuri domin Neman duba akan lamarin.

Sai dai mun tuntubi Wanda aka cire daga cikin jagororin Kungiyar NURTW ta Kasa Reshen jihar Kano, Wanda kuma, Mataimakin Shugaba ne a Kungiyar NURTW Bus 9 dake Tashar Malam Kato wato,Alh. Abdullahi Isah, dangane da wannan lamari na Kungiyar NURTW ta jihar Kano, Inda yace,ya godewa Allah Subahanahu Wata’ala da ya bashi damar hidimtawa alummar jihar Kano a cikin tsawon lokacin da ya rike mukamin Ma’ajin Kungiyar NURTW da yadda Alummar jihar Kano Suke ta yaba masa bisa gudunmawa da yake bayarwa ga Direbobi tun daga Kananan Hukumomi zuwa jiha da sauran Makwaftan jihohi na Kudu da Arewa da gabas da kuma yamma akan duk Abubuwan da suka taso.

Sai muka tambayesa akan batun Makudan Kudaden daya kashewa Gwamnati mai ci da Kungiyoyi a lokacin yakin Neman zaben kafa Gwamnati da kungiyoyin harkokin Sufuri domin ganin sun tsaya da kafafuwansu?

Abdullahi Isah ya bayyana cewa, ba wai yayi hakan domin Neman wasu Abubuwa ba,Sai don hidimtawa alummar Najeriya musamman na jihar Kano,wajen ganin jihar ta kara bunkasa ta fannin harkokin Sufuri da Kasuwanci da Tattalin Arziki,inda ya jaddada cewar,don an fitar da shi daga cikin jagororin Kungiyar NURTW ta Kasa Reshen jihar Kano, ba zai fasa taimakawa alummar jihar Kano ba,Domin jihar Kano ita ce a zuciyarsa.

Daga karshe Abdullahi Isah, ya Shawarci Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf,daya kara sanya idanu a fannin harkokin Kungiyoyin Sufuri da Sufurin baki daya domin samarwa Matasan Direbobi na jihar Kano Sana’oin dogaro da kai, Da ma yin gogayya da sauran jihohin Kasar nan.

Share188Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Fadar Shugaban Kasa Ta sake watsa kasa a idon masu murnar an Bude Boda

Next Post

Bayan bude bodojin Najeriya, kasar Niger ta rufe iyakokin ta da Najeriya

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Fadar shugaban kasa ta fadi dalilin Tinubu na tafiya China da iyalansa

Fassarar kalaman shugaban kasa

August 4, 2024
Majinyata A Najeriya Sun Koka Kan Yadda Magunguna Suka Yi Tsada A Fadin Kasar

Majinyata A Najeriya Sun Koka Kan Yadda Magunguna Suka Yi Tsada A Fadin Kasar

January 27, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

IPMAN Ta Nemi Dangote Ya Fara Kai Man Fetur Kai Tsaye zuwa Arewacin Najeriya

August 23, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media