Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Mai Zaman Kanta ta Najeriya (IPMAN) ta roƙi Dangote Refinery da ta faɗaɗa tsarin kai man fetur kai tsaye zuwa jihohin Arewacin Najeriya.
IPMAN ta ce hakan zai taimaka wajen samar da farashi iri ɗaya na man fetur a faɗin ƙasarnan, tare da rage tsadar sufuri da kuma sauƙaƙa wa masu amfani da man fetur wahalar tsadar rayuwa.
Ƙungiyar ta bayyana cewa samar da man fetur kai tsaye zuwa Arewa zai rage dogaro da safarar man daga kudancin ƙasar, wanda ke ƙara kuɗin da masu siya ke biya a gidajen mai.









