• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Majinyata A Najeriya Sun Koka Kan Yadda Magunguna Suka Yi Tsada A Fadin Kasar

aksam by aksam
January 27, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LAFIYA
ADVERTISEMENT
470
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA

Kamuwa da rashin lafiya a Nijeriya ya zama kalubalen da za a iya cewa ruwan dare, amma samun jinya da magani kuma sai su zama babban kakanikayi sakamakon tsadar magunguna da ‘yan Nijeriya da dama ba su iya saye.

RelatedPosts

Najeriya Sama Da 4,600 Ne Suka Koma Kasashen Waje Da Aiki A Cikin Shekaru 3 ‎ ‎—Rahoto

Wata Likita Ta Mutu Bayan Ta Haifi Ƴan-Uku; A Lokaci Daya

Matar Da Ta Haifi ‘Ya ‘Ya Biyar A Asibitin Murtala Ta Rasu

Tsadar magungunan musamman wadanda ake amfani da su yau da gobe irinsu rigakafi, maganin suga, ciwon kai, mura, maleriya da sauran cutukan da jama’a ke yawan fama da su na yau da kullum, abun da kawai majinyatan ke iyawa shi ne tururuwa zuwa asibitoci domin neman waraka.

Tsadar kayan magunguna babban barazana ne da ke fuskantar yawaitan zuwa asibitoci domin neman jinya, lamarin da ke neman a gaggauta daukan matakin shawo kansa domin kauce wa yawaitar mace-macen majinyata sakamakon rashin kudi ko kasa sayen magunguna.

Aksam Media ta ruwaito cewa Majinyata da dama sun nuna halin da suke ciki na mawuyacin yanayi musamman wadanda suke fama da karamin karfi kuma ba su cikin shirin inshuran kiwon lafiya, kamar wata uwa, Idowu Akinyemi wacce take fama da ciwon suga, ta shiga mamaki lokacin da ta je sayen magungunanta bisa gano yadda maganin ya yi tashin gwauron zabi farad daya

“Lokacin da na sayi maganina na karshe shi ne, naira dubu 3,000, amma yanzu maganin da na je shagon sayar da magunguna ya kai naira 5,000,” Idowu ta nuna damuwarta kan tashin magungunan.

Dokun Bolarinwa, mai fama da ciwon hawan jini, ya ce, yana kan magani da jinya a kowani lokaci, amma tsadar magungunan sannu a hankali ya sanya shi kauce wa ka’ida da dokokin da likita ta dora shi a kai.

“Ni tsohon ma’aikaci ne ba na da wata hanyar samun kudi a kowani lokaci. ‘Yan shekaru, ina ta fama da jinyar da ke damuna tare da gudunmawar ahlina, amma a ‘yan kwanakin nan gaskiya lamuran sun mana wuya. Na koma tsallake ranakun shan magani domin ba mu iya sayen maganin a kowani lokaci.”

Ade Ogun, wanda ya sayo maganinsa, sai dai ransa a bace cikin damuwa ya yin da ya gano cewa maganin da yake amfani da shi ya tashi, “Na sayi maganina a baya kan kudi naira 500, amma da na koma ya tashi da kaso 100, na yi matukar mamakin tashin maganin har haka,” Ade ya shaida.

Funmi Olaoye, matar aure ce wacce uwa ce kuma, da take jinyar danta mai fama da ciwon Asma, ta ce, “Yarona yana matukar bukatar kulawar magani kan ciwon asma da yake fama da shi, amma ba na iya sayen rashin maganin da ya dace na saya saboda tsada,” ta koka

Share188Tweet118SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yadda aka ceto wani matashi daga fadawa wuta akan bashi na miliyan biyu

Next Post

Yadda hukumar Hisbah tayi holen Direbobin adaidaita sahu 52

aksam

aksam

RelatedPosts

Najeriya Sama Da 4,600 Ne Suka Koma Kasashen Waje Da Aiki A Cikin Shekaru 3 ‎ ‎—Rahoto
LAFIYA

Najeriya Sama Da 4,600 Ne Suka Koma Kasashen Waje Da Aiki A Cikin Shekaru 3 ‎ ‎—Rahoto

by aksam
April 22, 2026
Wata Likita Ta Mutu Bayan Ta Haifi Ƴan-Uku; A Lokaci Daya
LAFIYA

Wata Likita Ta Mutu Bayan Ta Haifi Ƴan-Uku; A Lokaci Daya

by aksam
April 16, 2026
Matar Da Ta Haifi ‘Ya ‘Ya Biyar  A Asibitin Murtala Ta Rasu
LAFIYA

Matar Da Ta Haifi ‘Ya ‘Ya Biyar A Asibitin Murtala Ta Rasu

by aksam
March 26, 2026
INEC Ta Saka Ranakun Zaɓen 2027
LAFIYA

‎Muhimman Sauye-sauyen Da Aka Samu a Dokar Zaben Nijeriya

by aksam
February 19, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

China na kausasa martani kan kasar Amurka

January 14, 2024
Sarkin Musulmi Ya Bayyana Dalilansa Na Cewa Najeriya Tana Kan Tsini

Sarkin Musulmi Ya Bayyana Dalilansa Na Cewa Najeriya Tana Kan Tsini

February 15, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media