Daga: Hassan Umar Gwammaja
Rahotanni daga Jihar Kano sun tabbatar da rasuwar matar nan da ta haifi jarirai biyar a Asibitin Kwararru na Murtala.
Majiyoyi sun bayyana cewa matar, wadda ta haihu a jiya, ta rasu ne a daren Laraba bayan da aka ce tana karbar kulawar likitoci sakamakon yanayin haihuwar da ta bukaci kulawa ta musamman.
Rasuwar ta zo ne cikin yanayi mai tada hankali, musamman ganin yadda labarin haihuwar jariran biyar ya dauki hankalin al’umma a jihar da ma kasa baki daya.
Ya zuwa yanzu, ba a samu cikakken bayani daga hukumomin lafiya ba kan ainihin musabbabin rasuwar, yayin da ake sa ran za a fitar da karin haske kan lamarin.
A halin yanzu, hankula sun karkata kan lafiyar jariran biyar din, wadanda ake ci gaba da kula da su a asibitin.












