• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

‎Muhimman Sauye-sauyen Da Aka Samu a Dokar Zaben Nijeriya

aksam by aksam
February 19, 2026
Reading Time: 5 mins read
0
Home LAFIYA
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Cutar mashako

Governor Yusuf commissions Kano center for disease control

Shirin Gwamnatin Kano Na Kula Da Lafiyar Baki Ya Amfanar Da Mutane sama da 15,000

 

‎Daga: Hassan Umar Gwammaja
‎
‎Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan ƙudurin dokar zaɓen ƙasar na 2026, wanda aka yi wa gyaran fuska.
‎
‎Shugaban ya sa hannu kan dokar – wadda ta ƙunshi ƙa’idojin yin zaɓukan tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukumomin yankin birnin tarayya – ne ranar Laraba a Abuja, gaban manyan jami’an gwamnati.
‎
‎A lokacin sanya hannu kan dokar, Tinubu ya ce “babu batun siyasa a cikin wannan gyare-gyaren. Abu ne na tsari. Ƙoƙari ne na cike giɓi da ƙarfafa tsari da kuma samar da tsaftatacciyar hanya ga masu tsarawa da kuma masu yin zaɓuka.”
‎
‎Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar ne kwana ɗaya bayan hargitisn da aka samu a zaurukan majalisar tarayyar ƙasar game da amincewa da gyaran da aka yi wa dokar.
‎
‎Dokar wadda majalisar dattijai da ta wakilai suka amince da ita a ranar Talata ta bayar da damar tura sakamako daga rumfunan zaɓe ta na’ura da kuma ta takarda kamar yadda aka saba, ta yin amfani da fom ɗin EC8A.
‎
‎Amincewa da dokar na zuwa ne bayan doguwar muhawara game da saɗara ta 60, wadda ke magana kan tsarin da za a bi wajen tura sakamako daga rumfar zaɓe zuwa ga rumbun tattara sakamakon zaɓen hukumar Inec, wato IRev.
‎
‎A ranar Talata majalisar wakilai ta bi ra’ayin majalisar dattijai wajen amincewa da yin amfani da na’ura da kuma yin amfani da takardar da aka saba wajen tura sakamakon.
‎
‎Sashin ya bayar da dama ga jami’an hukumar Inec su yi amfani da takardar tura sakamako idan na na’urar ta gaza.
‎
‎
‎Muhimman sauye-sauye da ke cikin dokar zaɓen
‎
‎
‎Majalisar dattijan ta yi gyara ga saɗara ta 28 ta dokar zaɓen, inda ta rage lokacin fitar da tsare-tsaren zaɓe daga kwana 360 zuwa 300.
‎
‎Wannan ya bai wa hukumar zaɓen Najeriya damar tsara yin zaɓuka tsakanin watannin Disamban 2026 zuwa Janairun 2027.
‎
‎Wani ɓangare na saɗarar ta 28 da aka yi wa gyaran fuskar ta ce “Hukumar za ta wallafa tsare-tsaren yin zaɓe kwana 300 kafin ranar da za a gudanar da zaɓe a ƙarƙashin wannan doka, ta wallafa sanarwa na kowace jiha da kuma yankin Babban birnin tarayya”.
‎
‎Haka kuma majalisar dattawan ta yi gyara a sashi na 28 na kundin dokar zaɓe, inda ta rage wa’adi fitar da sanarwar zaɓen zuwa kwana 300, maimakon 360.
‎
‎Wannan ya sa hukumar INEC ke da ƴancin saka ranar zaɓe a tsakanin watan Disamban 2026 zuwa Janairun 2027.
‎
‎Wurin da aka gyara ya koma, “INEC za ta ayyana sanarwar lokacin zaɓe a jihohi da babban birnin tarayya Abuja a kwanakin ba su yi ƙasa da kwana 300 ba.”
‎
‎Haka kuma ƴan majalisar sun amince da gyaran ne bayan shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ya ce bayan nazarin dokokin, wa’adin kwana 360 da yake cikin sashi na 28 zai sa dole a gudanar da zaɓen a cikin azumin baɗi, wanda a cewarsa hakan ya kamata a yi gyara.
‎
‎Ya ce gudanar da zaɓe a lokacin Ramadan zai iya shafar zaɓen, domin mutane da dama ba za su sami damar zuwa zaɓen ba.
‎
‎Haka kuma ƙudurin ya buƙaci a yi nazari ɓangarori iri su 6, 9, 10, 22, 23, 28, 29, 32, 42, 47, 51, 60, 62, 64, 65, 73, 77, 86, 87, 89, 93, da 143.
‎
‎Haka kuma majalisar ta rage wa’adin miƙa sunayen ƴan takara zuwa kwana 120 maimakon kwana 180.
‎
‎Sannan dole Inec ta fitar da sunayen ƴan takara da ta tantance a cikin aƙalla kwana 60 kafin zaɓe maimakon kwana 150 da yake a baya
‎
‎Haka kuma an ɓarje-gumi kan lokacin gudanar da zaɓen, musamman inda Sanata Opeyemi ya buƙaci a dakatar da amincewa da gyare-gyaren da aka yi, a koma kwamiti a sake dubawa.
‎
‎Ya ce lokacin da INEC ta sanar domin gudanar da zaɓen na watan Fabrairun 2026 ya samu suka daga wasu masu ruwa da tsaki, inda ya ce ya saɓa da wa’adin aƙalla kwana 360 kafin ƙarewar wa’adin waɗanda suke mulki.
‎

‎Sanatan mai wakiltar Ekiti ta Tsakiya ya ce wa’adin na aƙalla kwana 360 wanda yake ƙunshe a sashe na 28, zai iya tilastawa a gudanar da zaɓen mai zuwa a cikin Ramadan.
‎
‎Haka kuma ƴan majalisar sun gano wasu saɓani a wasu wurare da dama na kundin, ciki har da sashe na 6, 9, 10, 22, 23, 28, 29, 32, 42, 47, 51, 60, 62, 64, 65, 73, 77, 86, 87, 89, 93, da 143.
‎
‎Rikita-tikita a majalisar wakilai
‎Tun da farko, an samu rikita-rikita a ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu, bayan ƴan majalisa sun nuna rashin amincewa da wasu ɓangarorin dokar zaɓen.
‎
‎Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan dokoki da tsare-tsare, Francis Waive ne ya gabatar da ƙudurin buƙatar majalisar ta janye matsayarta ta farko kan yanayin aiksa sakamakon zaɓen domin amincewa da tsarin da majalisar dattawa ta amince da shi.
‎
‎Da shugaban majalisar Tajudeen Abbas ya buƙaci a gudanar da ƙuri’ar murya, sai muryar nuna rashin amincewa ta fi ƙarfi, amma shi sai ya ce ta masu amincewar ce ta amo.
‎
‎Hakan ya sa wasu ƴan majalisar suka nuna rashin amincewa.
‎
‎Ƴan majalisar sun ci gaba da nuna rashin amincewarsu har suka fito harabar majalisar suna bayyana rashin jin daɗinsu.
‎
‎Sun bayyana buƙatarsu ta lallai sai an tabbatar da aika sakamakon zaɓen kai-tsaye ta intanet daga akwatunan zaɓe zuwa shafin intanet na IREV na hukumar INEC.
‎
‎An ji lokacin da masu zanga-zangar suke ta ihuce-ihucen cewa, “ba za mu amince ba, Akpabio ka amince da buƙatarmu,” kamar yadda suka bayyana.
‎
‎Wasu kuma cewa suka riƙa yi, “dole a yi amfani da ƙuri’armu.”

‎Shugaba Tinubu Ya Sanya Hannun Kan Dokar Zaɓe ta 2026

‎Ita dai tun da farko, majalisar dattawa ta amince a riƙa aika sakamakon zaɓen ne kai-tsaye ta intanet, amma a wuraren da babu intanet ta amince a yi amfani da takardu a rubuta sakamakon.
‎
‎Amma ita majalisar wakilai sai ta nace cewa dole a tabbatar da an aika sakamakon ta intanet ne kawai kai-tsaye, lamarin da ƙungiyoyi masu sa ido suka bayyana da wani matakin da zai rage maguɗi.
‎
‎Matsayar guda biyu mabambanta sun haifar da ce-ce-ku-ce, lamarin da ya sa majalisar dattawa ta shiga taron gaggawa domin gudanar da gyare-gyare.
‎
‎A lokacin ne Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya kafa kwamitin mutum 12 domin zama da ƴan majalisar wakilai domin haɗa rahotannin majalisun biyu wuri ɗaya.
‎
‎Yanzu dai an amince da cewa za a riƙa aika sakamakon zaɓen ne kai-tsaye daga akwatin ɗaya ta intanet, amma a wuraren da babu intanet mai kyau, za a iya amfani da takardar EC8A domin rubuta sakamakon zaɓen, sannan baturen zaɓe da wakilan jam’iyya ko ƴan takara suka sa hannu

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Kano: An Rufe Gidajen Gala da Harkokin DJ Har Zuwa Karshen Azumi

Next Post

The Ghana Tourism Authority Paid a Working Visit To Assess The Usability Of The Paragliding landing Site in Kwahu West Ahead of This Year’s Easter Festivities

aksam

aksam

RelatedPosts

Cutar mashako
LAFIYA

Cutar mashako

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Governor Yusuf commissions Kano center for disease control
LAFIYA

Governor Yusuf commissions Kano center for disease control

by Khadija Maitaya
August 4, 2026
Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Ginin da Ya Janyo Ce-ce-ku-ce a Unguwar Dorayi, Kano
LAFIYA

Shirin Gwamnatin Kano Na Kula Da Lafiyar Baki Ya Amfanar Da Mutane sama da 15,000

by Khadija Maitaya
July 22, 2026
An Kama Wata Matashiya Mai Shekaru 27 Bisa Zargin Satar Jariri A Asibiti A Zamfara
LAFIYA

An Kama Wata Matashiya Mai Shekaru 27 Bisa Zargin Satar Jariri A Asibiti A Zamfara

by aksam
May 17, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

The Best Way to Get Started at raceup casino

April 22, 2025
ECOWAS, bayan karewar wa’adin Tinibu Ana tunanin Kara masa wa’adi Akan wani dalilin guda daya tak

ECOWAS, bayan karewar wa’adin Tinibu Ana tunanin Kara masa wa’adi Akan wani dalilin guda daya tak

July 7, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media