Rahotanni sun bayyana cewa a yau Lahadi ne wa’adin shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS ya zo karshe.
Mun ruwaito cewa mambonin shugabannin ECOWAS sun amince da Tinubu a matsayin shugaba a babban taronta karo na 63 a kasar Guinea-Bissau.
Jaridar Tribune ta ruwaito cewa ana kan gudanar da taron ECOWA na 65 a fadar shugaban kasa dake Abuja inda ake sa ran zai Tinubu zai mika mulki ko kuma ya nemi tazarce.
Taron wanda aka shirya fara shi da karfe 11:00 na safe ne ake sa ran shugabannin ECOWAS za su zabi sabon shugaban da zai jagoranci harkokin kungiyar a shekara mai zuwa.
Sai dai jaridar The Punch ta ce akwai alamu da ke nuna cewa shugabannin na iya tsawaita wa’adin Tinubu domin ba shi lokaci dawo da kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso cikin kungiyar.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa da ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin yin magana a kan lamarin ta shaida wa jaridar cewa:












