Majalisar wakilai ta bukaci ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta gurfana a gabanta.
Rahotanni sun nuna cewa majalisar ta gayyaci Kennedy ne bisa zargin badakala da ta faru a ma’aikatar mata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu daga cikin ma’aikatan da suke ma’aikatar mata sun yi bayani kan halin da ake ciki.
Majalisar wakilai ta bayyana cewa ta gayyaci ministar matan ne saboda zargin karkatar da kudi Naira 1.5bn na yan kwangila.
Bincike ya nuna cewa yan kwangilar ne suka tura korafi ga majalisar bayan sun gama aiki ga ma’aikatar kuma ba a biya su ba, rahoton Leadership.
Shugabar kwamitin binciken, Kafilat Ogbara ta ce ma’aikatar mata ta fara wasu ayyuka da ba su cikin kasafin kudin shekarar 2023 bayan karkatar da N1.5bn.
Kafilat Ogbara ta kara da cewa ma’aikatar ta fara wasu ayyuka a jihohi 15 da sayen Keke NAPEP guda bakwai ga sojoji duk da cewa ana binta bashi.
Saboda haka majalisar ta bukaci dakatar da dukkan ayyukan da ma’aikatar ta fara har sai an samu bahasi kan yadda ma’aikatar ta kashe kudin da aka tura mata.










