Daga Hassan Umar Gwammaja
Likita mai suna Ere Ogbachi ta mutu ne a Jihar Bayelsa.
Jaridar Punch ta rawaito cewa bayan ta haihu lafiya a Asibitin Jami’ar Niger Delta, sai jikin ta ya rikice wanda ya sa aka garzaya da ita zuwa sashen kula da rashin lafiya mai tsanani (ICU) a Cibiyar Kwararo Ta Gwamtin Tarayya Dake Babban Birnin Yenagoa, inda da misalin karfe 2:45 na safiyar jiya Talata, ta ce ga garin ku nan.
Dangin ta sun bayyana cewa likitoci sun yi iya kokarinsu don ceton rayuwarta, amma ta shiga wani mawuyacin hali ne, inda daga ƙarshe ta cika.
PunchPunch ta ce Ere ta mutu ta bar sana’a+santalan jariran mata guda uku rigis, lamarin da ya jefa yan uwan ta da mai gidan ta cikin alhini.
Politics











