Hukumar kashe gobara ta jihar kano ta sami nasarar ceto wani matashi da ya yi yunkurin rataye kansa.
Lamarin ya faru a jiya Alhamis, akan titin gidan gwamnatin kano daura da gidan sarki, na cikin Rukunin gidajen Nasarawa.
Inda matashin me suna Saifullahi Rabi’u, mazaunin unguwar Samaigu yayi yunkurin rataye kansa, saboda wata matsala da ta faru dashi.
A cewar matashi Saifullahi ” na dauki wannan mataki ne a sakamakon yadda kudin wasu da nayi wa jagorancin yi wa bisa amma aka sami matsala”.
Lamarin daya kai ga masu kudin sun matsa min akan lallai na biya su kudin su kimanin naira milyan biyu kuma har na fara basu dubu 500, sai naga gwara na dauki wannan mataki, a cewar matashi Saifullahi.
Tuni Hukumar kashe gobara ta jihar kano, ta mika matashin ofishin ‘yan sanda dake Fam santa domin yin abin da ya kamata.










