Daga; Hassan Umar Gwammaja
Majalisar Dokokin ta sanya ranar Litinin 27 ga Afrilu, 2026 ne, domin tantancewa wanda ake so nada a matsayin mataimakin gwamna, Hon. Murtala Sule Garo
Shugaban Majalisar, Rt Hon. Jipbrin Ismaila Falgore, ne ya bayyana ranar tantancewar, bayan karanta wasiƙar neman amincewa da nadin da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aike wa majalisar a zaman zauren majalisa na ranar Laraba
Ana sa ran majalisar za ta gudanar da cikakken bincike kan cancanta da kwarewar Murtala Sule Garo kafin yanke hukunci kan amincewa da nadin nasa.










