Kungiyar masu kasuwancin kayayyaki Sawa ta mazan kwarai dake kasuwar Kantin kwari a jihar Kano ta yabawa Gwamna Abba Kabir Yusif bisa ayyukan ci gaba da yake a fadin jihar Kano, musamman bangare ilimi da gyara gyaren hanyoyin da suka lalace.
Shugaban Kungiyar Usman Sulaiman Wanda sakatarensa Alh. Rabiu Abubakar ya jagoranta ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Manama labarai a ofishin Kungiyar dake kasuwar Kantin kwari.
Rabiu Abubakar yace, Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya taimakawa ‘ya’yan talakawa da wanda ma ba talakawa ba wajen Kai dalibai kasashen wajen domin yin karatu kamar kowa, Wanda Yanzu sun Zama manyan mutane,masamman a bangare lafiya.
Sakataren ya jaddada cewar Kungiyar mazan kwarai dake kasuwar Kantin kwari tana baiwa Gwamnatin jihar Kano cikakken hadin Kan daya kamata domin bayyana ayyukan da Gwamnatin jihar ta yi abubuwa ci gaba ga alummar Kano.
Sakataren ya kuma bayyana cewar Yanzu lokaci yayi da Gwamnatin jihar Kano za ta Kara bibiyar ‘yan jamiyya domin tallafa musu da jarin da za su habaka kasuwancinsu ta hanyar bibiyar kungiyoyin da suke bata gudunmawa, musamman yankasuwa Wanda a cikin Kashi Dari na Samar da Gwamnatin jihar Kano,’yankasuwa na daga cikin wadanda suka ba da gudunmawa kwarai da gaske, Inda yace yakamata Gwamnatin jihar Kano ta tuna da kungiyoyin kasuwanni da suka je yakin kafata.
Shugabancin Kungiyar karkashin jagaranci Alh Usman Sulaiman yace yabawa Daraktan yada labaran Gwamnan Alh. Sunusi Bature Dawakin Tofa dangane da Yadda yake taimakawa ”yan yakinsa ta hanyar ba da jari ga matasa domin su dogara da kawunansu da ba da kayayyakin Noma da rabawa ‘yan karkara jakuna da motoci da babura domin ganin sun dogara da kawunansu.
Ya bayyana cewar,bisa wannan tagomashi ba za su manta da kyawawan Abubuwa da yake yi a yankunan Kano ta Arewa domin ciyar da alummar gaba.
Yace, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bargeshi bisa aikace -aikace da yayi a bangaren Kananan hukumomi na yakin, a Don haka Kungiyar take Kira ga Gwamnatin jihar Kano da ta tallafawa Kananan yankasuwa da Basu da jarin da za su yi Sana’a domin rage masu zaman kashe wando da masu kwacen wayoyin alumna Wanda wani lokacin ma har ta Kai da kisa Ko raunata mutum .
Daga karshe Shugaban Kungiyar masu kasuwancin kayayyaki Sawa ta mazan kwarai dake kasuwar Kantin kwari Alh. Usman Sulaiman yace Kungiyarsu a kodayaushe tana tare da wannan Gwamnatin Kuma kofar Kungiyar a Bude take domin tattarawa da Gwamnatin Akan Yadda za a horars da matasa sanin ilimin kasuwanci domin rage yawan masu shaye shayen muggwan kwayoyi da kwacen wayoyin alumna a matsayin neman kudade.
COV/I S GAMA/











