ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS

RelatedPosts

 

 

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sake jaddada jagorancinta a harkokin gudanar da aikin Hajji, inda ta bayyana cikakken shiri na jigilar maniyyata zuwa Ƙasa Mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.

Shugaban Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ƙaddamar da shirin allurar rigakafi ga maniyyata a Asibitin sansanin Alhazai na Jihar Kano.

Matawalle ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarar kammala bayar da biza kashi ɗari ga dukkan maniyyatan da suka nemi aikin hajjin bana, yana mai cewa wannan nasara alama ce ta ƙudurin Gwamnatin Jihar Kano wajen samar da ingantattun ayyuka da kula da jin daɗin al’ummarta.

Matawalle ya jaddada cewa an tanadi dukkan muhimman shirye-shirye, ciki har da na sufuri, takardu, da kuma matakan lafiya, domin tabbatar da cewa jigilar maniyyatan za ta gudana cikin sauƙi, tsaro, da nasara ba tare da wata matsala ba.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da mayar da hankali wajen samar da aikin Hajji mai sauƙi da cike da armashi na ibada ga dukkan maniyyatan jihar.

A na ta jawabin,Daraktar a Hukumar Kula da Lafiya a Tashoshin Shiga da Fita ta Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya Dr.Bilkisu Jibiril Idris ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano da shugabancin Hukumar Jin Daɗin Alhazai bisa kyakkyawan tsari da bin ƙa’idojin lafiya, inda ta bayyana shirin rigakafin a matsayin abin koyi, tana mai cewa Kano ta fi sauran jihohin da ta ziyarta tsari, haɗin kai da ƙwarewa a yayin da ake gudanar da allurar rigakafi ga maniyata.

 

ADVERTISEMENT

RelatedPosts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

ADVERTISEMENT

Trending.