Daga: Hassan Umar Gwammaja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya mayar da martani ga masu sukar gwamnatinsa, inda ya ce waɗanda ba sa ganin nasarorin da ake samu na iya buƙatar “tabarau” domin fahimtar ci gaban da ake samu.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban ya jaddada cewa gwamnatinsa na samun ci gaba a fannoni daban-daban, duk da suka daga wasu ɓangarori.
Kalaman nasa sun jawo martani a tsakanin jama’a, inda wasu ke goyon bayan maganar, yayin da wasu ke ci gaba da sukar yadda gwamnati ke tafiyar da al’amura.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan nasarori da ƙalubalen gwamnatin Tarayya.












