Kutun daukaka kararrakin zabe dake zaune a Abuja ta tabbatar da nasarar da Yusif Datti na jam’iyar NNPP yayi a zaben dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kura Madobi da garun Malam.
Jaridar solacebace ta ruwaito cewa kotun daukaka kara ta rushe hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta gudanar a birnin Kano, inda ta baiwa Musa Iliyasu Kwankwaso na jam’iyyar APC nasarar.
Tun da fari Musa Ilyasu Kwankwaso ya nuna rashin gamsuwarsa ne da ayyana Yusif Datti da INEC tayi inda ya garzaya kotun sauraron kararrakin zabe.









