• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Labaran yamma tareda khadija Muhammad maitaya

aksam by aksam
November 6, 2023
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
476
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, ta kammala sauraron ƙarar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya ɗaukaka, kan hukuncin kotun ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar.

Gwamnan dai yana ƙalubalantar hukuncin watan Satumba, wanda ya ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara, bayan kotun ta rage ƙuri’un Abba Kabir, sama da 160,000.

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

Bayan sauraron lauyoyin duka ɓangarorin, sai kotun ta ce ta ajiye hukunci, wanda ake sa ran za ta sanar kan wannan shari’a a ƙasa da mako biyu.

Babban lauyan gwamnan Kano, Wole Olanipekun ya roƙi kotun ta ba da damar sauraron ƙarar da suka ɗaukaka, sannan ta jingine hukuncin ƙaramar kotu gaba ɗayansa.

Ya yi iƙirarin cewa ƙaramar kotun ta ƙirƙiro wani sabon abu, wanda ya saɓa wa duk hukunce-hukuncen da kotun ɗaukaka ƙara, da Kotun Kolin ƙasar suka taɓa yankewa a baya.

Ya kuma ce hukuncin ƙaramar kotun kuskure ne, saboda wannan ne karon farko da wata jam’iyya a Najeriya, ta shigar da ƙara ba tare da ta sanya ɗan takararta a ƙorafin da ta yi ba, kuma duk da haka aka ayyana ɗan takarar a matsayin wanda ya yi nasara.

Sai dai babban lauyan jam’iyyar APC Akin Olujimi, ya ƙalubalanci matakin inda ya ce Kotunan Daukaka Kara sun yanke ƙarara cewa, rashin sa hannu a kan ƙuri’un da aka kaɗa, daidai yake da tafka maguɗin zaɓe.

Ya ce ƙa’idojin INEC sun zartar da abin da baturen zaɓe zai yi a rumfar kaɗa ƙuri’a, ciki har da tabbatar da sa hannu da kwanan wata a bayan kowacce ƙuri’a.

Ya ce a duk inda aka samu gazawar baturen zaɓe wajen yin abin da ya dace, hakan na iya zama an saɓa wa kundin dokar zaɓe.

Game da ɗan takarar APC wanda ba a sanya shi cikin ɓangarorin da ke cikin shari’ar a ƙaramar kotu ba, Mai shari’a Akin Olujimi ya ce tabbatacciyar doka ce cewa jam’iyya ake zaɓa a duk wani zaɓe da aka yi, kuma duk wani hukunci da ya shafi jam’iyyar siyasa, to ba shakka zai shafi duk ‘ya’yanta.

Share190Tweet119SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Yusif Datti na jam’iyar NNPP

Next Post

Yadda zaman jaruman tiktok da hukumar Hisbah ya wakana a jihar Kano

aksam

aksam

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa  ƴar Tik-tok  Dake Unguwar  Ɗanbare A Jihar Kano
LABARAI

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

by aksam
June 20, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

by Khadija Maitaya
June 19, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

by Khadija Maitaya
June 16, 2026
China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI
LABARAI

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

by Khadija Maitaya
June 14, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Sabuwar Jam’iyyar ADC A Najeriya Ta Naɗa Sanata David Mark A Matsayin Shugaban Tana Riƙo

Sabuwar Jam’iyyar ADC A Najeriya Ta Naɗa Sanata David Mark A Matsayin Shugaban Tana Riƙo

July 2, 2025
Ko kun san dalilan Shugaba Tinubu na sasanta rikicin siyar jihar Ondo

Ko kun san dalilan Shugaba Tinubu na sasanta rikicin siyar jihar Ondo

November 26, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media