Kotun tsarin mulkin kasar Uganda ta amince da dokar hana luwadi da ta ba da damar yanke hukuncin kisa duk da Allah wadai da kungiyoyin kare hakkin danadam da sauransu ke yi a kasashen turai.
Shugaba Yoweri Museveni shi ne ya sanya hannu kan dokar a watan Mayun bara. Wasu da dama a kasar ta gabashin Afirka na goyon bayan dokar, inda wasu ke ganin luwadi a matsayin dabi’ar da aka shigo da ita daga kasashen turawa kuma ba yanayin halitta ne na ainihi ba.
Wani dan fafatuka mai shigar da kara ya sha alwashin daukaka kara zuwa Kotun Koli.
Alkalan kotun tsarin mulkin kasar sun ce majalisar ta tabbatar da dokar ne bisa ka’ida kuma ba ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar ba. Dama luwadi laifi ne a Uganda a ƙarƙashin dokar zamanin mulkin mallaka wadda ke ayyana fasikanci da zina a matsayin laifi wanda ya saba ma “yanayin halitta.” Hukuncin wannan laifin shi ne daurin rai da rai.
Wanda ake tuhuma da laifin “yunkurin yin luwadi” za a iya daure shi har na tsawon shekaru 14, kuma laifin “yunkurin luwadi” yana da hukuncin shekaru 10.
Sai dai kotun ta ce kada a rika nuna wa ‘yan luwadi wariya yayin da suke neman waraka.
Kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana rashin jin dadinsa da hukuncin kotun, ya kuma yi kira ga gwamnatin Uganda da ta soke dokar.
Bankin Duniya ya dakatar da sabbin lamuni ga Uganda, yana mai cewa daukar karin matakan sun zama dole don tabbatar da cewa ayyukan da bankin ke yi sun yi daidai da irin muhalli da kuma zamantakewar da bankin ke amincewa da su.












