• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yadda kungiyar IS ta kai mummunan hari a wata kasar Africa

aksam by aksam
April 4, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Rundunar sojin Congo ta ce ‘yan tawayen masu nasaba da tsattsauran ra’ayi sun kashe akalla mutane goma sha biyu a wani samame da suka kai a wani kauye a gabashin kasar, a tashin hankalin na baya bayan nan a kusa da kan iyaka da Uganda.

‘Yan tawayen Allied Democratic Forces masu alaka da kungiyar IS sun dade suna kai farmaki a yankin kan iyaka. Majalisar Dinkin Duniya ta ce a makon da ya gabata an kashe kusan mutane 200 a wannan shekara.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Kaftin Anthony Mulushayi, kakakin rundunar sojojin Kongo a lardin Kivu ta Arewa, a ranar Talata ya ce maharan da safiyar wannan rana sun kona wani asibitin yankin tare da kora wasu fararen hula zuwa daji. Ya ce sojojin sun mayar da martani inda suka kashe hudu daga cikin maharan tare da ceto mutane hudu.

Wani shugaban farar hula na yankin, Kakule Mwendapeke, ya ce adadin fararen hula da abin ya rutsa da su ya zarta haka, inda aka kashe akalla mutane 17, ciki har da yara hudu ‘yan kasa da shekaru 10. Wasu mutane 15 kuma sun bace bayan an yi garkuwa da su, in ji Mwendapeke. Wadanda suka tsira sun tsere daga kauyukansu don neman mafaka a wasu biranen da ke kusa da su ciki har da Beni da Mangina.

Yankin na gabashin Kongo dai ya shafe shekaru da dama yana fama da tashe-tashen hankula yayin da sama da kungiyoyi 120 dauke da makamai ke fafutukar ganin sun mallaki albarkatun ma’adinai masu mahimmanci, wasu kuma na kokarin kare al’ummominsu. ‘Yan tawaye na yawan kashe jama’a. Rikicin ya sa sama da mutane miliyan bakwai kaurace wa gidajensu, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Bintou Keita, babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya a Kongo, ta yi gargadi a makon da ya gabata cewa tashe-tashen hankula na kara ta’azzara, inda aka samu rahoton cin zarafin dubban mutane da suka hada da fyade da cin zarafin mata a bana.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Kin aiwar da dokar auren jinsi, Bankin Duniya ya soke lamuni ga wata kasa

Next Post

Bazoum, Kotu ta baiwa shugaban kasar Niger zazzafan umarni

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Saukar karatun Al’qur’ani Dari 600

April 8, 2024
Tun Kafin Ranar 1 Ga Watan August Ta Zo Domin Fara Zanga-Zangar Lumana;  Wasu Jihohin Sun Fara

Tun Kafin Ranar 1 Ga Watan August Ta Zo Domin Fara Zanga-Zangar Lumana; Wasu Jihohin Sun Fara

July 30, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr. Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media