• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Bazoum, Kotu ta baiwa shugaban kasar Niger zazzafan umarni

aksam by aksam
April 4, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Wata kotu a birnin Yamai ta umurci hukumomin tsaro a jamhuriyar Nijar su gaggauta sakin wasu makusantan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum daga inda ake tsare da su.

Alkalin kotun yace ana tsare da wadanan mutane ne ba akan ka’ida ba kuma jinkirin mutunta wannan hukunci abu ne da zai ja wa gwamnatin kasar biyan tarar miliyan 1 na cfa a kowace rana har zuwa lokacin da za a bai wa wadanan mutane damar komawa cikin iyalinsu.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Tun a ranar da hukumomin mulkin sojan Nijar suka zargi hambararren Shugaban kasa Mohamed Bazoum da yunkurin tserewa daga inda yake tsare ne jami’an tsaro suka kama Abdourahamane Ben Hamey da Mohamed M’Barek a jerin mutanen da ake zargi da hannu a abinda aka kira yunkurin tada hankalin kasa da yi wa hukuma barazana.

An ja lokaci mai tsawo ba tare da jin duriyar wadanan mutane ba kafin daga bisani a gano cewa suna tsare a wani ofishin jamia’n tsaron Jandarma dake birnin Yamai lamarin da ya sa lauyoyinsu shigar da kara a kotu domin ta dubi abin da suka kira take doka da tauye hakkin bil adama.

Bayan nazari akan bahasin bangarorin biyu a zamanta na talata 2 ga watan Afrilu, kotun ta umurci hukumomi su salami wadanan mutanen.

Yace Doka ta kayyade cewa bai kamata a fice wata 1 a na tsare da mutun ba tare da an gabatar da shi gaban alkali ba. su kuma wadanan mutane sun shafe watanni 6 da mako 2 a ofishin jandarmomi abin da ke nufin ana tsare da su ne ba akan ka’ida ba.

Domin tabbatar da cewa an bi umurnin Kotun alkalin dake wannan shari’a ya gindaya wa mahukunta sharadi inji Maitre Djibo.

Yace za ta yiwu hukumomin Nijar su yi ta jan kafa kokuma su ki zartar da hukuncin kotun. matakin da ke biyo bayan aikata wannan dabi’a ta kin sakin wadanan mutane shine biyan tarar miliyan 1 na cfa a kowace rana har zuwa lokacin da komai zai je daidai.

Kawo yanzu ba wani martani daga bangaren gwamnatin Nijar wace ma’aikatar Agence Judiciare de L’etat ke wakilta a wannan shara’a koda yake hukuncin kotun na cewa akwai damar daukaka kara kafin nan da makwanni biyu masu zuwa.

A saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yadda kungiyar IS ta kai mummunan hari a wata kasar Africa

Next Post

Shugaba Tinubu Zai Bar Abuja A Gobe Lahadi Zuwa Legas Don Yin Bikin Karamar Sallah

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero; Ya Jajintawa Tsohon Gwamnan Shekarau

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero; Ya Jajintawa Tsohon Gwamnan Shekarau

May 7, 2024
Shettima Ya Nemi Kada A Yi Masa Tallan Taya Murna Kan Cikarsa Shekara 60

Shettima Ya Nemi Kada A Yi Masa Tallan Taya Murna Kan Cikarsa Shekara 60

August 29, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media