• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Bayan yanke hukuncin kano Zamfara pilato bangaren sharia ya fara farfado da kimar sa: wani babban lauya

aksam by aksam
January 14, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
468
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Masana harkokin siyasa da shari’a a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da hukunce-hukuncen da kotun ƙolin ƙasar ta yanke game da zaɓen gwamnonin jihohi bakwai na ƙasar.

Wasu masana fannin shari’a na ganin hukunce-hukuncen sun farfaɗo da martabar ɓangaren shari’a na Najeriyar.

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Wani lauya mai zaman kansa a birnin Abuja, Dakta Umar Mainasara Ibrahim Kogo, a zantawar sa da BBC hausa ya ce ya kamata a yaba wa ɓangaren shari’ar ƙasar saboda hukunce-hukuncen sun taimaka wurin inganta martabar ɓangaren a idon al’umma.

‘Sun fara la’akari da cewa akwai giɓi tsakanin yawancin hukunce-hukuncen da suke yankewa da kuma yadda jama’a ke karɓarsu, musammman yadda suke dogara kan abubuwa marassa muhimmanci da ke danne ainihin zallar gaskiya idan aka zo maganar shari’a’. In ji shi.

Ya ƙara da cewa alƙalan sun yi ƙokari saboda ba su bari ka’idojin zaɓe sun shafe dokokin ƙasa ba, kuma sun hana a ɗauko wasu al’amuran da ba su shafi tsarin mulki da dokar ƙasar ba domin kawo cikas a harkokin shari’a.

Ya ce, ”alƙalai ya kamata su ɗauki kansu a matsayin wakilan al’umma wurin wanzar da adalci da gaskiya, ta ƙokarin tabbatar da cewa ba a yi amfani da dabarun lauyoyi wurin danne wa masu gaskiya haƙƙinsu ba.’

Dakta Mainasara ya yi kira ga hukumar zaɓen ƙasar da ta tashi tsaye wurin tsabtace yadda take gudanar da al’amuranta domin a rage aukuwar kura-kurai a ɓangaren zaɓe.

A ɓangaren masana siyasa, Farfesa Abubakar Umar Kari da ke jami’ar Abuja ya bayyana cewa hukunce-hukuncen kotun ƙolin za su taimaka wurin ƙarfafa dimokraɗiya a ƙasar.

Ya ce, ‘abin da dimokuraɗiya ta tanadar shi ne kowanne ɓangare ya yi aikinsa, hukumar zaɓe za ta gudanar da zaɓe ta kuma ayyana waɗanda suka yi nasara. Su kuma waɗanda ba su gamsu da wannan sakamakon ba dimokuraɗiya ta ba su damar cewa su kai ƙara kotu, ita kuma kotu ta saurari ƙara ta kuma yanke hukunci. Kuma a nawa ganin waɗannan hukunce-hukuncen sun sami karaɓuwa.’

Farfesa Kari ya ce dole ne a samu waɗanda hukuncin kotu ba zai yi masu daɗi ba, amma idan har an yi adalci wurin yanke hukunci kuma jama’a sun amince da hukuncin da kotu ta yanke, hakan zai taimaka wurin ƙara ƙarfafa dimokuraɗiya a ƙasar.

‘Ni dai a ganina mafi yawan waɗannan jihohi, waɗanda aka ayyana cewa sun ci zaɓe, akwai alamun cewa su ne al’umma suka zaɓa. su waɗanda suka kai ƙara suna son ne su sami nasara kan waɗansu hujjoji na shari’a, amma ba wai a kan cewa su ne suka ci zaɓen ba.’

Waɗannan masana da wasu daga al’ummar Najeriya na fatan cewa ɓangaren shari’ar ƙasar zai ci gaba da ɗaukar matakan da suka kamata domin kauce wa duk wani lamari da ka iya haifar da shakka da za ta shafi ƙimarsa da kuma tabbatar da adalcin da ake tsammani daga gare shi a kodayaushe.

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Sojojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga 86 a wani samame

Next Post

China na kausasa martani kan kasar Amurka

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Kalli asarar da masu zanga-zanga suka yi a babbar kotun jihar Kano bayan sace takardun da ake tuhumar Ganduje

Kalli asarar da masu zanga-zanga suka yi a babbar kotun jihar Kano bayan sace takardun da ake tuhumar Ganduje

August 14, 2024
Yadda hukumar Makarantar shahada ta gabatar da shawarwari ga Dalibai

Yadda hukumar Makarantar shahada ta gabatar da shawarwari ga Dalibai

October 2, 2023
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

Kotu Ta Yanke Wa Matar Aure Hukunci Bayan Samunta Da Watsa Tafasasshen Ruwa Ga Kishiyarta

August 7, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media