Hukumar kula da ingancin kayan abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta gargadi masu gidajen Burodi su daina amfanida Danzaki da sauran kayan da ke cutar da mutane a cikin Burodi.
Shugaban hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, shi ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi ga kamfanin Dillancin labarai na kasa NAN.
Ya ce duk gidan burodin da suka samu da kunnen kashi ga wannan gargadi zai girbi abin da ya suka.
Ya ce ma’aikatan su na fita rangadi lokuta daban-daban sabo da yawan korafe korafe da suke samu a ofishin su na rashin inganta Burodi da abin da ya kamata.










