Ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasa (IPMAN), ta ce mambobinta ba sa samun lodin Man fetur a matatar Mai ta Aliko Dangote duk da cewa sun biya naira Bilyan 40 ga kamfanin NNPCL.
Shugaban IPMAN, Abubakar Garima ne bayyana hakan a zantawar sa da tashar Channels, inda ya ce sun yi mamaki da suka ji Dangote yana cewa dillalan man fetur ba sa zuwa matatarsa sayen mai.
A cewar sa, “Idan zai sayar da mai kai-tsaye za mu saya saboda dole sai mun biya za’a ba mu man, duba da yanzu haka akwai kuɗinmu naira Bilyan 40 a wajen NNPCL amma ba ma samun kayan.
A kwanakin nan wasu Motocin mambobinmu da NNPCL ta tura matatar Dangote, suka kwashe kwana huɗu a can ba tare da sun samu man ba.
A ƙarshe IPMAN ta yi kira ga Dangote da ya duba farashin man matatarsa, sannan ya kwatanta da farashin man na ƙasashen waje, kana ya bincika lokacin da fetur din ke ɗauka kafin ya isa ga dillalin.
A jiya Talata ne dai Dangote ya ce yana da litar mai sama da Milyan 500 a ajiye, amma dillalan man ba sa sayen fetur ɗin nasa.












