Mai girman gwamnan jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya umarci jamiar Ado Bayaro BUK da ta gaggauta tsayar da gine-ginen da take gudanar wa a garin Rimin Danzakara.
Gwamnan ya yi umarnin ne cikin wata sanarwa da Mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a jiya Alhamis
Sanarwar ta samu ne sanadiyar rikicin da ya barke tsakanin mazauna garin Rimin Danzakara da jami’an tsaro na BUK wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka uku tare da jikkata wasu da dama.
Kungiyar Kwadago ta NLC Ta Dakatar Da Zanga-zangar Adawa Da Karin Farashin Kudin Kira Da Na Data
Jamiyar PDP ta zargi tsohon gwamnan Kano da haifar mata da nakasu a tafiyar ta
A ziyarar gani da Ido da yakai gwamnan ya yi ta’aziya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su tare da alkawarin daukar nauyin su da Gina masallacin Juma’a sadaukar wa ga mazajansu.
A bangaren wadanda suka jikkata gwamnan ya yi alkawarin gwamnati zata kula da lafiyar su tare da Kai ayyukan more rayu da suka hada da wutar lantarki da tuka-tuka na Sola da hanya zuwan garin na Rimin Danzakara.











