Daga Hassan Umar Gwammaja
Yan Sandan Kano Sun Tabbatar Da Rasuwar Mutane 2 Sanadiyar Fadan Daba.

Rundunar ta samu Yan Sandan jahar Kano, ta tabbatar da Rasuwar mutane 2, biyo bayan fadan Daba da Ake Zargin wasu matasa daga unguwannin , Zango da kuma Kofar Mata.
Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da Jaridar Idongari.ng , a shelkwatar Rundunar dake unguwar Bompai Kano.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce tun a ranar Lahadi, suka samu kiraye-kiraye daga unguwar Kofar Mata , daidai lokacin da aka tashi wasa a filin wasa na Sani Abacha Stadium, Inda wasu matasa suka dinga yin fadace-fadacen daba Tsakanin Unguwa da Unguwa.
” Bisa rahotannin da muka samu an ce mana fadan Daba ne Tsakanin unguwar Zango da kuma Kofar Mata” cewar SP Abdullahi Haruna Kiyawa “.
Kiyawa ya kara da cewa bayan Samun rahotannin marasa Dadi kwamishinan yan Sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya Tura dakarun Yan Sanda da gaggawa wajen da lamarin ya Faru , kuma sun Samun rahotan Mutuwar mutane 2.
Rundunar ta ce yanzu haka an dukufa wajen gudanar da bincike don ganin duk Wanda yake da Hannu akan fadace-fadacen dabar, ya zo don ya fuskanci hukunci.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa ayau Litinin , Rundunar ta kara Tura dakarun Yan Sanda, bayan samu wasu kiraye-kirayen don ganin an Yi abunda yakamata don wanzar da zaman lafiya.
A karshe Rundunar taja hankalin al’umma, musamman wajen taimaka wa jami’an Yan Sandan da bayanan sirri, tunda dai wadanda suke aikata laifukan Yan unguwane.











