Babban mataimaki ga gwamnan jihar kano akan harkokin kananan hukumomi ,hon Bashir A Yaro ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa dake maaikatar kananan hukumomi a sakatariyar audu bako dake nan kano,hon Bashir yace gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin,Engr Abba kabir Yusif zata inganta shelikwatar kananan hukumomi arba’in da hudu wajen gyara su,domin dawo dasu hayyacinsu daga Yadda suka zama kufai.babban mataimakin ya godewa daukacin maaikatan maaikatar kananan hukumomin musammam babban sakataren hukumar da daraktoci
Sannan ya Kuma bukaci alumar jahar kano dasu cigaba da Bawa gwamnatin hadin Kai da goyon baya










