Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya shigar da ƙara a gaban kotu, inda yake ƙalubalantar majalisar dokokin jihar kan zarge-zargen da ta yi masa na almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin mulkinsa.
Gwamnan ya shigar da ƙarar ne a ranar Laraba a wata babbar kotun tarayya da ke birnin Kaduna.
Wata sanarwa da tsohon gwamnan ya fitar ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labaru, Muyiwa Adekeye, ta ce Elrufa’i ya shigar da ƙarar ce domin tabbatar da haƙoƙoƙin da yake da shi na kare kai game da binciken da majalisar dokokin jihar ta ce ta yi a kansa.
Lauyan El-Rufa’i, AU Mustapha ya ce tsohon gwamnan ya ɗauki matakin ne ganin cewa yana da hakkin a saurare shi a duk wani mataki na bincike ko kotu da za a ɗauka kansa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Saboda haka El-Rufa’i ya buƙaci kotun ta ayya rahoton kwamitin majalisar dokokin jihar kan binciken ayyukan gwamnatinsa a matsayin haramtacce, wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki kuma ya saɓa wa tanadin kundin tsarin mulki na jin ta-bakin wanda ake zargi.
Dama dai tsohon gwamnan ya yi watsi da rahoton kwamitin, inda ya bayyana shi a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.
Cikin wata sanarwa da Muyiwa Adekeye ya fitar a madadinsa, El-Rufai ya ce ya bauta wa Kaduna “da gaskiya kuma yana alfahari da abubuwan da ya yi”.
“[El-Rufai] ya bi duk wasu dokoki a ayyukansa lokacin da yake gwamna…ya kamata a yi watsi da wannan binciken na ƙeta a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.”










