Daga: Hassan Umar Gwammaja
Sakamakon rashin nasarar da kungiyar ta yi a wasan karshe na Gasar Zakarun Turai da PSG.
Sai dai har yanzu babu cikakkiyar sanarwa daga hukumomi da ta tabbatar da cikakken bayani kan lamarin.
Lamarin, wanda aka ce ya faru a yankin Amakohia Ubi da ke karamar hukumar Owerri West, ya jefa iyalai da mazauna yankin cikin jimami, tare da sake tayar da muhawara kan tasirin da sakamakon wasanni ke yi ga lafiyar kwakwalwa da tunanin wasu magoya baya.
Masana da masu fafutukar kula da lafiyar kwakwalwa na ci gaba da jaddada cewa duk da muhimmancin wasanni da farin cikin da suke kawowa, bai kamata sakamakon wasa ya kai ga yanke kaunar rayuwa ko daukar matakin da zai jawo asarar rai ba.
Sun bukaci mutane da su nemi taimako ko tattaunawa idan suna cikin damuwa ko matsin tunani mai tsanani.










