Wani sabon rahoto ya nuna cewa kashi 23.6 cikin 100 na gwaje-gwajen tantance uba da aka gudanar a Najeriya sun tabbatar da cewa yaran da ake zaton ’ya’yan wasu mazaje ne, ba nasu ba ne.
Rahoton da ƙungiyar Smart DNA ta fitar kan bayanan shekarar 2025 zuwa 2026, ya nuna cewa kusan ɗaya daga cikin yara huɗu da aka yi wa gwajin tantance uba a cikin waɗannan gwaje-gwajen, ba su da alaƙar jini da mazajen da ake zaton su ne iyayensu.
Ƙungiyar ta ce wannan alkaluma na ƙara nuna muhimmancin gwajin DNA wajen tabbatar da hakikanin uba da kuma warware shakku da ka iya tasowa tsakanin ma’aurata da iyalai.
Shugabar Smart DNA, Elizabeth Digia, ta bayyana cewa yawancin mutanen da ke zuwa cibiyar domin yin gwajin ba wai wani ne ya tilasta musu ba, sai dai suna zuwa ne saboda ba za su iya ci gaba da rayuwa cikin shakku da zargin da ke damunsu ba.
Bayanan ɗakin gwaje-gwajen sun kuma nuna cewa gwajin DNA na tantance uba na taka muhimmiyar rawa wajen warware tambayoyi da wasu iyalai ba sa iya ko kuma ba sa son warwarewa ta hanyar tattaunawa kawai. Ƙungiyar ta yi kira ga ma’aurata da su ƙara bai wa amana muhimmanci, tare da amfani da gwajin DNA cikin hikima idan akwai buƙatar tabbatar da asali.









