• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Gwamnonin Arewa sun lashi takobin kawo karshen matsalar tsaro a yankinsu

aksam by aksam
June 26, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai rika tuntubar juna da aiwatar da abubuwan da aka cimma bayan, kammala taron inganta zaman lafiya da tsaro a yankin da aka gudanar a Katsina.

An gudanar da taron ne da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya inda ƙwararru da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro suka yi gagarumar tattaunawa ta kwana biyu tare da cimma matsaya kan abubuwa da dama wadanda za su taimaka wajen magance matsalar tsaron da ke addabar yankin.

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso yamman, kuma ya shaida wa BBC cewa taron ya sha banban da wadanda aka sha gudanarwa a baya.

Ya ce ganin irin fuskokin da suka halarci taron, hakan ya nuna musu cewar matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin ta dami kowa, wanda yasa mutanen da a baya suke yi wa lamarin ruƙon sakainar kashi, yanzu kowa ya fahimci cewar dole ne a haɗa hannu wajen ganin an ɗauki matakai da za su kawo ƙarshen matsalar

“Mun faɗa wa juna gaskiya mu gwamnoni ga kurakuren mu, kowa ga nasa, sannan ga yadda muke ganin ya kamata a magance wannan matsala, haka su ma Majalisar Dinkin Duniya sun gaya mana ga yadda suke ganin za a shawo kan matsalar, mun kalli mastalolin a bayyane” inji shi.

Kungiyar gwamnonin Arewa maso yammacin Najeriya da hadin guiwar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya suka shirya taron wanda aka kammala a ranar Talatar da ta gabata, wanda aka gudanar a jihar Katsina.

Cikin masu halartar taron har da mataimakin shugaban kasa Khashim Shatima da manyan jami’an tsaro da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Shugaban Jami’ar Usman Danfodio Farfesa Saidu

Next Post

Zargin Almundahna takaddama ta kai ga kotu tsakanin El-Rufa’i majalisar dokokin Kaduna

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Vavada kazino spēļu tips un unikālās iezīmes

October 26, 2023

Digitālā azarta nākotne: inovācijas un tendences tiešsaistes kazino industrijā

April 21, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media