• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Shugaban Jami’ar Usman Danfodio Farfesa Saidu

aksam by aksam
June 25, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Mataimakin Shugaban Jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato, Farfesa Yusuf Saidu.

Wmaiakin Shugaban Jami’ar wanda farfesa ne a fannin ilimin halitta da kwayoyin halittu, yana kan hanyar sa daga Sokoto zuwa Kaduna ne lokacin da ‘yan bindigan suka kai hari su ka kashe shi a kan hanyar Gusau zuwa Funtua.

Da yake tsokaci kan kisan, mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Suleiman Bilbis ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai rikon amana da addini, da kwazo, da jajircewa.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto jami’an tsaro ba su ce yi wani bayani ba da lamarin ba, sai dai Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo ta sanar da rasuwar a wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook da yammacin jiya Litinin cewa, “Mutuwar tasa babbar asara ce ga al’ummar jami’a da kuma duniyar ilimi. Allah ya karbi ransa, ya gafarta masa zunubansa, amma wannan rashi ne mai zafi ga daukacin jama’ar jami’a da kuma jami’a baki daya.”

Ana ta aika sakonnin ta’aziya ga iyalan marigayin da kuma jami’ar Usmanu Danfodiyo kai tsaye da kuma ta kafofin sadarwa. Sheikh Abdurrahman Umar Bagarawa ya wallafa a shafinsa na facebook cewa, “Wallahi na firgita da mutuwar nan!… Kwanaki uku da suka shige, nake maganarsa da Mal. Abdul-Alim Isa T/Mafara, har nake cewa ya turo min nambar wayarsa, ashe Allah bai nufa zamu yi ganawa ta karshe ba! Mutumin kirki da riko da addini. Allah ya gafarta masa!”

Shi kuwa Professa Isa Ali Pantami tsohon Ministan sadarwa cewa ya yi “Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, VC, Farfesa Bilbis, al’ummar jami’a, ‘yan uwa da abokan arziki, tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya shigar da shi Jannatul Firdausi.”

Dandalin yanar gizo na malaman jihar Katsina shi kuma ya wallafa cewa, “Allah ya karbi ransa ya gafarta masa zunubansa, amma wannan rashi ne mai radadi ga daukacin jama’ar jami’a da fannin ilimi baki daya. Allah ya jiqanshi ya karbi shahadarshi, Allah ya shiryi masu irin wannan aika-aikan, in ba masu shiryuwa bane, ya Allah ka hukunta su bisa qaddarawar ka ya Rabb Amin. Innalillahi Yanzu shike nan mutum mai amfani mai amfànar da Al’umma an kashe shi haka kawai?.”

A nata sakon jajen, kungiyar daliban sashen nazarin halittu ta wallafa cewa, “Hakika mun yi rashin uba da kuma mai ba da shawara a fannin ilimi Farfesa Yusuf Saidu DVC na fannin nazari da fasaha,kuma daya daga cikin kwararrun malamai da muke da su a sashen nazarin halittu da kwayoyin halitta da ke Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato. Ina rokon Allah Ta’ala Ya sa Jannatul Firdausi ce makomarsa ta karshe.”

Idan dai za a iya tunawa, wasu ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da wasu masu bautar kasa 12 a watan Agusta bara, da ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Akwa Ibom a hanyar Gusau zuwa Funtua, kuma har yanzu daya daga cikinsu yana hannun ‘yan ta’addar.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Tsananin Zafi Ya Halaka Ɗaruruwan Alhazai A Hajjin Bana A Saudiyya

Next Post

Gwamnonin Arewa sun lashi takobin kawo karshen matsalar tsaro a yankinsu

aksam

aksam

RelatedPosts

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta
LABARAI

Sarkin Zurmi Ya Rasu Bayan Shekaru Biyar A Kan Sarauta

by Khadija Maitaya
September 1, 2026
Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute
LABARAI

Kano State Govt ends 50 year BUK/Rimin zakara Land Dispute

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Yaki da harkar Daba a Jihar Kano

by Khadija Maitaya
August 31, 2026
Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo
LABARAI

Babban Malami Ya Kalubalanci Gwamnoni da ’Yan Majalisa Bisa Rufe Cibiyoyi 10 Na Yin Fasfo

by Khadija Maitaya
August 30, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Bayan Gaza biyan Miliyan 248 KEDCO ta yanke wutar lantarkin Jami’ar Aliko Dangote

Bayan Gaza biyan Miliyan 248 KEDCO ta yanke wutar lantarkin Jami’ar Aliko Dangote

July 1, 2024

Yunƙurin kisa Kalli yadda wani shugaba ya shiga hannun rundunar yan sanda

January 23, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

Masu Siye Da Siyar Da Filaye A  R/zakara Sunkoka Da Aibantasu Da Gwamnatin Kano Keyi.

August 26, 2026
Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

Cristiano Ronaldo Ya Auri Georgina Rodríguez

August 12, 2026
Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

Wani Kauran Mata Ya Jikkata Wata Dattijuwa Bayan Ta Hana Shi Shiga Gurin Da Bai kamata Ba

August 29, 2026
Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

Masu Zuba Jari 40+ daga Masar na Sha’awar Zuba Jari A Najeriya

August 23, 2026
Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

Iran Ta Kakkabo Wasu Manyan Jiragen Yaƙi Na Amurka

August 14, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media