• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Tsananin Zafi Ya Halaka Ɗaruruwan Alhazai A Hajjin Bana A Saudiyya

aksam by aksam
June 20, 2024
Reading Time: 5 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA

Adadin wadanda suka mutu a aikin Hajji na bana da aka yi a kasar Saudiyya sakamakon yanayin tsananin zafi ya haura 900.

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

Wani jami’in diflomasiyyar Larabawa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Laraba cewa mutanen da suka mutu a cikin alhazan Masar kadai sun haura zuwa “aƙalla 600” daga sama da 300 a rana daya da ta gabata, galibi saboda tsananin zafin ranar da da wahala a jure masa.

Euro 2024: Potugal Ta Sha Da Kyar A hannun Jamhuriyar Chek

Adadin ya sa jumullar waɗanda suka mutu zuwa yanzu ya kai 922, kamar yadda alƙaluman da AFP ya tattara waɗanda ƙasashe da dama suka fitar suna nuna.

Daga baya jami’in diflomasiyyar ya ƙara da cewa jami’an Masar a Saudiyya sun kuma samu rahoton ɓatan alhazai,” ciki har da 600 da suka rasa rayukan nasu.

Mabrouka bint Salem Shushana ‘yar ƙasar Tunisiya, wadda ke cikin shekarunta na 70 ta ɓata tun a ranar hawan Arafa, kamar yadda mijinta Mohammed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Laraba.

Ya ce ba ta samu damar shiga wajen da aka tanada mai na’urar sanyaya waje ba saboda ba a mata rajista ba kuma ba ta da izinin yin Hajji.

“Ta tsufa. Ga shi kuma tagaji. Tana jin zafi sosai kuma babu wajen da za ta iya bacci,” ya faɗa.

“Na duba ta a duka asibitocin, Amma har yanzu babu alamarta.”

An yi ta watsa cigiyar hotunan waɗanda ba a gani ba a Facebook da sauran shafukan sada zumunta don samun bayanai.

Cikin masu neman bayanai har da ‘yan’uwa da ƙawayen Ghada Mahmoud Ahmed Dawood, wata ‘yar ƙasar Masar da ba a gan ta ba tun ranar Asabar.

“‘Yarta ta min waya daga Masar tana roƙona da na wallafa saƙo a Facebook wanda zai iya taimakawa a gano ta,” in ji wata ‘yar’uwarsu da take zama zama a Saudiyya.

“Abin daɗin dai shi ne har yanzu ba mu ga sunanta a jerin mutanen da suka mutu ba, wanda hakan ya sa muke fatan cewa tana raye.”

Houria Ahmad Abdallah Sharif mai shekara 70 ‘yar Masar ma ta ɓata tun ranar Asabar.

Bayan da ta kammala addu’a a kan Dutsen Arafa sai ta gaya wa ƙawarta cewa za ta je banɗaki don wanke abayarta, dawowar da ba ta yi ba kenan.

Aikin Hajji daya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar kuma duk Musulmin da yake da hali dole ne ya yi shi akalla sau daya. An ƙayyade lokacinsa bisa kalandar watan Musulunci, inda yake sassauyawa a kowace shekara a kalandar Miladiyya.

A cikin shekaru da dama da suka gabata, Hajjin kan faɗo a daidai lokacin bazara a Saudiyya.

Wani bincike na Saudiyya da aka wallafa a watan da ya gabata ya nuna cewa zafi na ƙaruwa da digiri 0.4 a ma’aunin salshiyas a kowace shekara 10.

Baya ga Masar, ƙasashen Jordan da Indonesiya da Iran da Senegal da Tunisiya da Iraƙi ma sun tabbatar da mutuwar mutanensu, ko da yake a lokuta da yawa hukumomi ba su bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.

Wani jami’in diflomasiyyar Larabawa na biyu ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a ranar Laraba cewa jami’an kasar Jordan na neman mahajjata 20 da suka ɓata, ko da yake wasu 80 da aka ce sun ɓace tun farko suna kwance a asibitoci.

Shi ma wani jami’in diflomasiyyar Asiya ya shaida wa kamfanin dilancin labaran AFP cewa akwai “kusan mutum 68 da suka mutu” daga Indiya kuma wasu sun ɓata.

“Wasu (sun mutu) ba tare da wata lalura ba, sannan muna da mahajjata da yawa da suka tsufa. Wasu kuma saboda yanayin tsananin zafi; abin da muke zato kenan,” in ji shi.

A bara ma fiye da alhazai 200 ne aka ba da rahoton mutuwarsu, mafi yawansu daga Indonesiya.

kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Laraba cewa mutanen da suka mutu a cikin alhazan Masar kadai sun haura zuwa “aƙalla 600” daga sama da 300 a rana daya da ta gabata, galibi saboda tsananin zafin ranar da da wahala a jure masa.

Euro 2024: Potugal Ta Sha Da Kyar A hannun Jamhuriyar Chek

Adadin ya sa jumullar waɗanda suka mutu zuwa yanzu ya kai 922, kamar yadda alƙaluman da AFP ya tattara waɗanda ƙasashe da dama suka fitar suna nuna.

Daga baya jami’in diflomasiyyar ya ƙara da cewa jami’an Masar a Saudiyya sun kuma samu rahoton ɓatan alhazai,” ciki har da 600 da suka rasa rayukan nasu.

Mabrouka bint Salem Shushana ‘yar ƙasar Tunisiya, wadda ke cikin shekarunta na 70 ta ɓata tun a ranar hawan Arafa, kamar yadda mijinta Mohammed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Laraba.

Ya ce ba ta samu damar shiga wajen da aka tanada mai na’urar sanyaya waje ba saboda ba a mata rajista ba kuma ba ta da izinin yin Hajji.

“Ta tsufa. Ga shi kuma tagaji. Tana jin zafi sosai kuma babu wajen da za ta iya bacci,” ya faɗa.

“Na duba ta a duka asibitocin, Amma har yanzu babu alamarta.”

An yi ta watsa cigiyar hotunan waɗanda ba a gani ba a Facebook da sauran shafukan sada zumunta don samun bayanai.

Cikin masu neman bayanai har da ‘yan’uwa da ƙawayen Ghada Mahmoud Ahmed Dawood, wata ‘yar ƙasar Masar da ba a gan ta ba tun ranar Asabar.

“‘Yarta ta min waya daga Masar tana roƙona da na wallafa saƙo a Facebook wanda zai iya taimakawa a gano ta,” in ji wata ‘yar’uwarsu da take zama zama a Saudiyya.

“Abin daɗin dai shi ne har yanzu ba mu ga sunanta a jerin mutanen da suka mutu ba, wanda hakan ya sa muke fatan cewa tana raye.”

Houria Ahmad Abdallah Sharif mai shekara 70 ‘yar Masar ma ta ɓata tun ranar Asabar.

Bayan da ta kammala addu’a a kan Dutsen Arafa sai ta gaya wa ƙawarta cewa za ta je banɗaki don wanke abayarta, dawowar da ba ta yi ba kenan.

Tsananin zafi

Aikin Hajji daya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar kuma duk Musulmin da yake da hali dole ne ya yi shi akalla sau daya. An ƙayyade lokacinsa bisa kalandar watan Musulunci, inda yake sassauyawa a kowace shekara a kalandar Miladiyya.

A cikin shekaru da dama da suka gabata, Hajjin kan faɗo a daidai lokacin bazara a Saudiyya.

Wani bincike na Saudiyya da aka wallafa a watan da ya gabata ya nuna cewa zafi na ƙaruwa da digiri 0.4 a ma’aunin salshiyas a kowace shekara 10.

Baya ga Masar, ƙasashen Jordan da Indonesiya da Iran da Senegal da Tunisiya da Iraƙi ma sun tabbatar da mutuwar mutanensu, ko da yake a lokuta da yawa hukumomi ba su bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.

Wani jami’in diflomasiyyar Larabawa na biyu ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a ranar Laraba cewa jami’an kasar Jordan na neman mahajjata 20 da suka ɓata, ko da yake wasu 80 da aka ce sun ɓace tun farko suna kwance a asibitoci.

Shi ma wani jami’in diflomasiyyar Asiya ya shaida wa kamfanin dilancin labaran AFP cewa akwai “kusan mutum 68 da suka mutu” daga Indiya kuma wasu sun ɓata.

“Wasu (sun mutu) ba tare da wata lalura ba, sannan muna da mahajjata da yawa da suka tsufa. Wasu kuma saboda yanayin tsananin zafi; abin da muke zato kenan,” in ji shi.

A bara ma fiye da alhazai 200 ne aka ba da rahoton mutuwarsu, mafi yawansu daga Indonesiya.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Muna Duba Yiwuwar Saka Dokar Ta Baci A Kan Barkewar Annobar Kwalara – Hukumar NCDC

Next Post

Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Shugaban Jami’ar Usman Danfodio Farfesa Saidu

aksam

aksam

RelatedPosts

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Ranar Talata 05 GA watan Mayu 2026, A Matsayin Ranar Da Zai Jagoranci Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan
LABARAI

by aksam
May 4, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
LABARAI

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

by aksam
May 4, 2026
NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano
LABARAI

NDLEA Ta Kama Mutane 6, Ta Rushe Maboyar Miyagun Kwayoyi a BUK Old Site Kano

by Khadija Maitaya
May 4, 2026
Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A  Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga  Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC
LABARAI

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar Haɗaka Ya ADC

by aksam
May 3, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Yadda Nana Akupo, ya nemi shugabannin Africa su dawo daga rakiyar masu Jan kunne

February 19, 2024
Inna lillahi wa Inna ilayhi raji’un!!!

Inna lillahi wa Inna ilayhi raji’un!!!

May 10, 2025
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Comr.  Usaini Sani Adamu !!!

April 24, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Umar SA’ID

April 20, 2026
Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

Shekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano

May 4, 2026
Muna Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Daurin Auren;- UMAR SA’ID

April 17, 2026
Atiku, Kwankwaso , Obi Sun Jagoranci Zanga-Zanga A Babban Birnin Tarayya Abuja

April 8, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media