• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Yadda Nana Akupo, ya nemi shugabannin Africa su dawo daga rakiyar masu Jan kunne

aksam by aksam
February 19, 2024
Reading Time: 2 mins read
0
Home LABARAI
ADVERTISEMENT
467
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya yi kira ga shugabanni da gwamnatocin kasashen Afirka da su hada kai, su dau matakin zuba hannun jari na kashi talatin cikin dari a cibiyoyin hada-hadar kudi na Afirka da nufin inganta ma’aunin wadannan cibiyoyi yadda za su tallafawa ci gaban Afirka.

Shugaba Akufo-Addo ya yi wannan kira ne a yayin jawabin da ya gabatar a taron shugabannin kasashe da na gwamnatocin Afirka da aka gudanar a taron shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka (AU) karo na 37.

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

Taron, wanda aka yi wa taken “Kafa cibiyoyin hada-hadar kudi ta Tarayyar Afirka a tsarin ajandar Afirka don sake fasalin tsarin hada-hadar kudi na duniya.”

Shugaban ya nuna cewa, a halin yanzu, dukkan kasashen Afirka suna ware kashi dari bisa dari (100%) na asusunsu na ketare ga cibiyoyin hada-hadar kudi da ke wajen Afirka, duk kuwa da cewa hakan ba ya kawo wani alfanu ga nahiyar.

Yace “dukkanmu mun yarda cewa yadda tsarin hada-hadar kudi na duniya ke aiki ba ya taimaka mana [Afirka], kuma akwai bukatar yin wasu muhimman sauye-sauye a tsarin. Amma yin hakan kuma na buƙatar mu [‘yan Afirka] mu ɗauki wasu matakai da za su taimaka mana wajen samun kudaden da za su tafiyar da tattalin arzikinmu”.

Shugaban ya kara da cewa, idan har aka samu hanyar kara karfin samun kudade ga cibiyoyin Afirka, to lallai an samu turbar samar da kudaden ci gaban Afirka.

Bincike da aka gudanar ya zuwa shekarar 2021, na cewa jimillar ajiyar kasashen Afirka dake kasashen waje ya kai kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.1.

Mai sharhi kan tattalin arziki da harkokin kudi, Hamza Attijjany yace “kudaden da ake ajiyewa a wasu bankuna, musamman a Turai; daloli ne, wasu kuma Yuro, wasu ma gwal ne ake ajiyewa. A duk lokacin da kasar ta shiga matsalar karayar darajar kudi ko kuma in kasar za ta yi cinikayya da kasashen waje sai a yi amfani da wadannan kudaden.”

Share187Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Ya Faɗa A Komar Hukumar EFCC Bisa Zargin Almundahana Biliyoyin Naira A Lokacin Mulkinsa.

Next Post

Matasan jam’iyyar APC sun barke da zanga-zanga saboda abu 1 tak

aksam

aksam

RelatedPosts

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa  ƴar Tik-tok  Dake Unguwar  Ɗanbare A Jihar Kano
LABARAI

Wani Matashi Ya Rasu A Gidan Budurwarsa ƴar Tik-tok Dake Unguwar Ɗanbare A Jihar Kano

by aksam
June 20, 2026
Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro
LABARAI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafafen Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro

by Khadija Maitaya
June 19, 2026
Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka
LABARAI

Sky News: Yaƙin Trump da Iran Na Daya Daga Cikin Manyan Kurakuran Dabarun Amurka

by Khadija Maitaya
June 16, 2026
China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI
LABARAI

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

by Khadija Maitaya
June 14, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Shugaba Bola Ahmad  Tinubu Ya Gana Da Peter Obi, Fayemi A Fadar Vatican

Shugaba Bola Ahmad Tinubu Ya Gana Da Peter Obi, Fayemi A Fadar Vatican

May 18, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi

Kotu Ta Yanke Wa Umar Idris Farawa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Bisa Samun sa Da Laifi

April 22, 2026
ADVERTISEMENT

Trending.

Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media