Jami’ar Aliko Dangote dake garin Wudil ta tsinci kanta cikin duhu biyo bayan Gaza biyan kudin wutar lantarki ga kamfanin rarraba wutar lantarki na jihar Kano.
Shugaban sashin walwalar Dalibai Farfesa Abdulkadir Danbazau ya ce lamarin ya faru ne kimanin sati guda da ya gabata inda kawo yanzu alamura da da a na makarantar ya Sami tasgaro.
A cewar sa sun yi kokarin shawo kan matsalar Amma lamarin yacitura
Cikin kokarin da suka yi ya hada da baiwa kamfanin KEDCO Miliyan 20 Dan shawo kan matsalar Amma ya ki amincewa ya mayar musu da wutar lantarki a makarantar.
A cewar sa rashin wutar lantarki babbar matsalace ga makarantar musamman kasancewarta Jami’ar kimiya da fasaha
Ya ce lamarin ya tilasta wa makarantar neman agajin gwamnatin Kano domi ta shigo cikin lamarin kafin a kai ga dawowar Dalibai daga hutu inda abin zai fi kamari.












