• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
AKSAM
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO
No Result
View All Result
AKSAM
No Result
View All Result

Iyalan Janar Rabe sun Musanta Sanarwar Gwamnatin Katsina Kan Dalilin Mutuwarsa

aksam by aksam
June 15, 2026
Reading Time: 1 min read
0
Home Uncategorized
ADVERTISEMENT
466
SHARES
1.5k
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga Hassan Umar Gwammaja

Ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayi Manjo Janar Abubakar Rabe mai ritaya, Isyaka Rabe, ya musanta ikirarin da gwamnatin Jihar Katsina ta yi cewa mahaifinsa ya rasu ne sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini.

RelatedPosts

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato

Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa

Zafin Rana Ya Hallaka Mutum 16 A Indiya

A wata hira da ya yi da Deutsche Welle (DW), Isyaka ya ce mahaifinsa bai taɓa fama da ciwon sukari ko hawan jini ba. Ya bayyana cewa wasu na zargin wataƙila ya mutu ne bayan maciji ya sare shi, bisa ga wani bidiyo na ƙarshe da masu garkuwa da shi suka fitar, amma ya ce Allah kaɗai ne ya san ainihin musabbabin mutuwarsa.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai ibada, son zaman lafiya da rayuwa mai sauƙi, yana mai cewa ya mutu a matsayin jarumi.

Isyaka ya kuma ce bai san yadda aka karɓo gawar mahaifinsa ba, yana mai cewa gwamnati ce kaɗai za ta iya yin bayani kan hakan.

Haka kuma ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa mahaifiyarsa, wadda aka sace tare da mahaifinsa, ta samu ‘yanci, yana mai tabbatar da cewa har yanzu tana hannun masu garkuwa da mutane.

A nata ɓangaren, ɗiyar marigayin, Adda Abubakar, ta wallafa a shafinta na X cewa mahaifinta bai da ciwon sukari, tana mai jaddada cewa cizon maciji ne ya yi sanadin mutuwarsa.

An sace Janar Rabe da matarsa ne a ranar 30 ga Mayu, 2026, a kan hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina. Daga bisani ya rasu yana tsare a hannun masu garkuwa da shi.

Sai dai gwamnatin Jihar Katsina ta ce marigayin ya mutu ne sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini, yayin da iyalansa da wasu majiyoyi ke cewa cizon maciji ne ya yi ajalinsa.

Share186Tweet117SendShare
ADVERTISEMENT
Previous Post

China Ta Soke Darussa 12,000 na Jami’o’i Domin Shirin Zamani na AI

Next Post

Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Nasarar Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Abubakar Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

aksam

aksam

RelatedPosts

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato
Uncategorized

Mahara Sun Kashe ’Yan Yawon Sallah Bakwai A Sakkwato

by aksam
June 2, 2026
Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa
Uncategorized

Rahotanni Daga Jihar Imo Sun Bayyana Cewa Wani Magoyin Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Arsenal Ya Rasa Ransa

by aksam
May 31, 2026
Zafin Rana Ya Hallaka Mutum 16 A Indiya
Uncategorized

Zafin Rana Ya Hallaka Mutum 16 A Indiya

by aksam
May 31, 2026
Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano Ta Dakatar Da Wasu Jaruman Kannywood Biyu
Uncategorized

Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano Ta Dakatar Da Wasu Jaruman Kannywood Biyu

by aksam
May 17, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recommended.

Dalilan kamfanin KEDCO na dauke wutar lantarki na tsawon awa 12 a gobe Lahadi

Dalilan kamfanin KEDCO na dauke wutar lantarki na tsawon awa 12 a gobe Lahadi

October 28, 2023
Rikicin sarauta: Yanzu haka wata babbar kotun tarayya na sauraron karar da Aminu Ado ya shigar

Rikicin masarauta: kotu ta ci tarar gwamnatin kano bisa take hakkokin Aminu Ado

June 14, 2024
ADVERTISEMENT

Trending.

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

An Kammala Gasar Kwallon Kafar Sada Zumunchi Dan Muna Murnar Zagayuwar Sallah Babba Cikin Nasara A Garin Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 1, 2026
Mu Na Gayyatar  ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

Mu Na Gayyatar ‘Yan Uwa Da Abokanan Arziki Zuwa Gurin Daurin Auren:- Ango Bulaye

June 12, 2026
The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

The Emir of Zangon Nkawkawo, Alhaji Abdul-Nasir Usman, Extends Eid Greetings

June 1, 2026
Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

Ga Sakon Bangajiya Daga: Angon Sha’ibu Sani Mai Atamfa (Bulaye)

June 15, 2026
Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da  Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma  A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

Irin Yadda Ake Cigaba Da Gudanar Da Karatun Saukar Al’qur’ani Mai Girma A Zango Nkawkawo Dake Kasar Ghana

June 5, 2026

Aksam Hausa

AKSAM MEDIA is a company which designed as online News Platform and other activities related to develop society.

The AKSAM MEDIA created since November 2019 and it does many activities as News publishes it publishes a Hausa News And English News.

No Result
View All Result
  • Home
    • KOTU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • KIMIYA DA FASAHA
  • LAFIYA
  • TSARO

© 2023 Aksam media