DAGA HASSAN UMAR GWAMMAJA
Tuni dai shugaban Kungiyar NARTO na kasa, Othman Yusuf, ya umarci mambobinsu da su dawo bakin aiki nan take a fadin kasar nan biyo bayan janye yajin aikin.
Matakin hakan na zuwa ne bayan shiga tsakani da Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur suka yi kamar hukukomin da ke kula da dokokin man fetur irinsu NNPCL, NMDPRA, DAPPMA da dai sauran su suka yi.
Da yake jawabinsa ga manema labarai bayan ganawar sulhun da ta gudana tun daga jiya zuwa maraicen yau na Talata, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Ekperipe Ekpo, ya ce kungiyar NARTO ta dakatar da yajin aikin gama-gari da ta shirya daga jiya litinin 19 ga watan Fabrairun shekarar 2024 da muke ciki.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, mambobin kungiyar NARTO dai sun dakatar da ayyukansu na jigilar man fetur a fadin kasar sakamakon tsadar man dizal da kuma matsin tattalin arziki a kasar nan.
Mambobin kungiyar NARTO sun yi barazanar tsayar da ayyukansu a fadin kasar tun daga jiya Litinin saboda tsadar man dizal, wanda ake amfani da shi wajen jigilar man fetur da motocinsu a fadin Najeriya baki daya.
Kamar man fetur wanda a yanzu ake sayar da shi daga kan Naira dari 6 zuwa 7 kan kowace lita, farashin man dizal ya yi tashin gwauron zabi a musamman a baya-bayan nan, lamarin da ba ya rasa nasaba da tashin farashin dala a kasuwannin bayan fagge da na hukuma a kasar.
A yanzu dai ana sayar da man dizal sama da Naira dubu daya da 250 duk lita a sassan Najeriya.
A don haka kowa ne jarumi ya tabbatar yaje ofishin kungiyar ta Mopan dake kan titin zuwa jami’ar Bayero, kusa da ofishin Ismail Khalil Jaen domin yin rijistar.











