Yan bindiga sun kai hari kauyukan manoma a kananan hukumomin Maradun da Tsafe da ke jihar Zamfara tun a ranar Alhamis din da ta wuce
Rahoto daga yankunandda abin ya shafa ya nuna cewa daga cikin waɗanda aka kashe har da wani babban malamin addinin Musulunci, Mallam Makwashi Maradun
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya tabbatar da kai hare-haren amma ya ce bayani zai biyo baya










